Ka dakatad da shirin daukan matasa 774,000 aiki - Yan majalisa sun bukaci Buhari

Ka dakatad da shirin daukan matasa 774,000 aiki - Yan majalisa sun bukaci Buhari

Majalisar dattawan Najeriya da na wakilai a jiya sun bukaci shugaba Muhammadu Buhari ya dakatad da shirinsa na daukan matasan Najeriya 774,000 aikin gyara a fadin tarayya.

Wannan bukata da yan majalisan suka mikawa Buhari ya biyo bayan rikicin da ya faru tsakanin kwamitin daukan aiki na majalisar da karamin ministan kwadago da aikinyi, Festus Keyamo.

Yan majalisan sun kalubalanci Festus Keyamo kan kwamitin mutane 20 da ya kafa don zaben wadanda za'a dauka aikin.

Yayinda yake kokarin bayani kan tambayar da sukayi masa, sai yan majalisan suka ce akwai bukatar a kebe gefe ba tare da yan jarida ba.

Shi kuma ministan ya ce sam bai amince a kebe gefe ba saboda ba zai yiwu a tuhumeshi a bainar jama'a kuma ya bada amsa a boye ba.

Ya ce ta wani dalili ake kokarin boyewa yan Najeriya gaskiya kuma idan basu shirya sauraronsa a gaban jama'a ba, zai fita daga wajen.

Ka dakatad da shirin daukan matasa 774,000 aiki - Yan majalisa sun bukaci Buhari
Ka dakatad da shirin daukan matasa 774,000 aiki - Yan majalisa sun bukaci Buhari
Asali: Facebook

KU KARANTA: 'Ba 'yan bindiga ba ne': An gano wadanda suka kai hari asibitin FMC Lokoja, an bayyana dalilinsu

Bayan tafiyarsa, yan majalisan sun tattauna kan yadda za su shawo kan lamarin.

The Nation ta samu labarin cewa bayan sun kwashe kimanin sa'o'i biyu sun tattaunawa, yan majalisan sun nuna bacin ransu kan abinda Minista Keyamo yayi.

Kakakin majalisar dattawa, Sanata Ajibola Basiru, da na wakilai, Hon. Benjamin Kalu, a jawabin da suka saki sun lashi takobin cewa sai an dakatad da shirin har sai an yiwa yan majalisa bayani yadda ake gudanar da shirin.

Gwamnatin tarayya ta bayyana sunayen dukkanin 'yan kwamitin da za su jagoranci ragamar shirinta na daukan matasa 774,000 aiki a duk jihohi 36 na kasar da kuma birnin Abuja.

Ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren kasa, Zainab Ahmed, ita ce ta sanar da hakan a ranar Litinin, 6 ga watan Afrilun 2020.

Duba jerin sunayen a nana https://hausa.legit.ng/1343739-gwamnatin-tarayya-ta-fidda-sunayen-yan-kwamitin-da-za-su-ja-ragamar-daukan-matasa-774000-a-duk-jihohin-najeriya.html

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng