'Ba 'yan bindiga ba ne': An gano wadanda suka kai hari asibitin FMC Lokoja, an bayyana dalilinsu

'Ba 'yan bindiga ba ne': An gano wadanda suka kai hari asibitin FMC Lokoja, an bayyana dalilinsu

Gwamnatin jihar Kogi ta fitar da jawabi dangane da harin da ake tunanin cewa wasu 'yan bindiga ne suka kai asibitin gwamnatin tarayya (FMC) da ke Lokoja, babban birnin jihar Kogi.

Da safiyar ranar Laraba ne wasu mutane da ake zargin 'yan bindiga ne su ka kai hari asibitin FMC Lokoja yayin da ake gudanar da taro a kan annobar korona.

Sai dai, gwamnatin jihar Kogi ta ce ba 'yan bindiga ne su ka kai harin ba.

A cewar gwamnatin, dangin wani marar lafiya ne suka kai harin sakamakon haushin da suka ji na rashin bawa marar lafiyar da suka kai kulawa.

Wadanda su ka kai harin sun yi awon gaba da na'urori ma su kwakwalwa, muhimman takardu, tare da lalata kayayyaki a asibitin.

Amma, a cewar kwamishinan yada labarai da harkokin sadarwa na jihar Kogi, Kingsley Fanwo, dangin marar lafiyar sun gudanar da zanga - zanga ne kawai a asibitin.

"Bincikenmu na farko - farko ya nuna cewa an samu hatsaniya a asibitin bayan dangin wani marar lafiya sun fusata sakamakon rashin basu kulawa a lokacin da suka kai dan uwansu bashi da lafiya.

'Ba 'yan bindiga ba ne': An gano wadanda suka kai hari asibitin FMC Lokoja, an bayyana dalilinsu
Wani bangare na asibitin da aka lalata
Asali: UGC

"Jama'a da dama a sashen neman taimakon gaggawa basu samu kulawar ma'aikatan asibitin ba, lamarin da ya sa har wata mai juna biyu ta haihu a bakin kofar asibitin. Hakan ya fusata jama'a da dama a jihar.

"Tun a jiya (Talata) 'yan uwa da dangin marasa suka fara damuwa bayan sun samu labarin cewa ma'aikatan asibitin za su gudanar da wata zanga - zanga domin neman kariya daga annobar korona.

DUBA WANNAN: Shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar Borno, Dakta Wakil, ya rasu

"Mu na kira ga jama'a a kan su kwantar da hankulansu, gwamnati za ta tabbatar da an yi wa doka biyayya.

"Bai kamata a siyasantar da harkar lafiya ba. Mu na kira ga ma'aikatan lafiya su cigaba da aikinsu na taimakon jama'a, gwamnati za ta basu kariya domin su samu sukunin gudanar da aikinsu.

"Gwamnati za ta kara zurfafa bincike domin sake gano wasu dalilai da suka tunzura jama'a har suka gudanar da zanga - zanga sannan za a warware duk wata damuwarsu," a cewar kwamishina Fanwo.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng