'Alfarma': Buhari ya ja kunnen hukumomi da ma'aikatun gwamnati

'Alfarma': Buhari ya ja kunnen hukumomi da ma'aikatun gwamnati

Shugaba Muhammadu Buhari ya sake ja kunnen Ma'aikatu, Hukumomi da Cibiyoyin gwamnatin da su dena sauraron masu neman alfarma wurin neman aiki ko kwangila da sauransu.

Gargadin na shugaban kasar tana kunshe ne cikin wata sanarwa da Ministan Labarai da Al'adu, Lai Mohammed ya fitar a ranar Laraba.

Sanarwar na dauke da sa hannun Segun Adeyemi, Mataimaki na musamman a fanin watsa labarai a Ofishin Ministan Labarai da Al'adu Lai Mohammed.

'Alfarma': Buhari ya ja kunnen hukumomi da ma'aikatun gwamnati
'Alfarma': Buhari ya ja kunnen hukumomi da ma'aikatun gwamnati. Hoto daga The Nation
Asali: UGC

Ministan ya ce Shugaban kasar ya yi gargadin ne bayan samun rahotanin cewa yan damfara na amfani da kati ko wasika da suke ikirarin sun samu daga hadiman shugaban kasa ko wasu manyan ma'aikata don neman alfarmar aiki ko kwangila.

DUBA WANNAN: Fitattun 'yan Najeriya 12 da suka rasu a watan Yuni

Shugaban kasar a cewar Ministan, ya jaddada cewa wannan halin ya ci karo da tsarin yadda wannan gwamnatin ke gudanar da ayyukan ta.

"Wannan gwamnatin ta tanadar da ingantattun hanyoyin da za a gudanar da ayyukan gwamnati ta yadda za a yi wa dukkan yan Najeriya adalci, ko wurin daukan aiki ko kwangila.

"Ya kamata a bari tsarin da aka tanada ya yi aikinsa ba tare da katsalandan daga wasu yan Najeriya ba," in ji shi.

A wani labarin daban, Gwamnan jihar Niger Abubakar Sani Bello ya bayar da umurnin rage albashin dukkan masu riƙe da muƙaman siyasa a jiharsa da kashi 30 cikin 100.

Wadanda za a rage wa albashin da allawus sun hada da Gwamnan da mataimakinsa, Kwamishinoni, mashawarta na musamman da sauran musu muƙaman siyasa.

Ragin albashin da allawus ɗin zai fara aiki nan take kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Hakan na cikin wata sanarwa ce da sakataren gwamnatin jihar, SSG, Ahmed Ibrahim Matane ya fitar.

Sanarwar ta kuma ce ragin albashin na wuccin gadi ne saboda illar da annobar Covid-19 ta yi wa tattalin arzikin jihar.

Gwamnatin za ta koma biyan albashi da allawus kamar yadda ta saba da zarar annobar ta wuce kuma tattalin arziki ya koma yadda ya ke.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel