Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun tarwatsa taron COVID-19 a asibitin Kogi

Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun tarwatsa taron COVID-19 a asibitin Kogi

'Yan bindiga a ranar Laraba sun kai hari Cibiyar Lafiya ta Tarayya, FMC, da ke Lokoja, Jihar Kogi inda suka tarwatsa taro a kan COVID-19 da ake gudanarwa.

Asibitin ta shirya yin taron manema labarai domin kira ga gwamnatin jihar ta samar da cibiyar yin gwajin COVID-19 a jihar kana ta tattauna kalubalen da ma'aikatan lafiya ke fuskanta a jihar saboda cutar.

The Cable ta ruwaito cewa yan bindigan sun isa asibitin cikin motoci guda uku inda suka fara harbe harbe da bindiga wadda hakan yasa mutane suka tarwatse.

Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun tarwatsa taron COVID-19 a asibitin Kogi
Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun tarwatsa taron COVID-19 a asibitin Kogi. Hoto daga Sahara Reporters
Asali: UGC

Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun tarwatsa taron COVID-19 a asibitin Kogi
Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun tarwatsa taron COVID-19 a asibitin Kogi. Hoto daga Sahara Reporters
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Fitattun 'yan Najeriya 12 da suka rasu a watan Yuni

Rahoton ya ce yan bindigan sun razana ma'aikatan lafiya inda suka kwace muhimman takardu da kwamfuta ta laptop daga hannunsu.

Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun tarwatsa taron COVID-19 a asibitin Kogi
Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun tarwatsa taron COVID-19 a asibitin Kogi. Hoto daga Sahara Reporters.
Asali: Facebook

Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun tarwatsa taron COVID-19 a asibitin Kogi
Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun tarwatsa taron COVID-19 a asibitin Kogi. Hoto daga Sahara Reporters.
Asali: Facebook

An kuma ce sun lalata wasu kayayyaki a asibitin.

Kawo yanzu Rundunar Yan sandan jihar ba ta riga ta yi tsokaci a kan afkuwar lamarin ba.

Ku saurari karin bayani ...

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164