Rikicin manoma da makiyaya: Mutum 9 sun rasu, 6 sun raunata a Bauchi

Rikicin manoma da makiyaya: Mutum 9 sun rasu, 6 sun raunata a Bauchi

- Mutane tara suka rasa rayukansu a Malunje da ke kauyen Zadawa a jihar Bauchi bayan rikicin da ya barke tsakanin manoma da makiyaya

- Al'amarin ya faru a ranar Litinin inda ya kai har sa'o'in farko na ranar Talata bayan wasu daga cikin masu fadan sun je daukar fansa

- Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Ahmad Wakili, ya tabbatar da aukuwar al'amarin amma ya ce tuni komai ya lafa

Mutum tara suka rasa rayukansu sannan mutum shida sun samu miyagun raunika a kan rikicin gona da ya barke tsakanin manoma da makiyaya a Malunje da ke kauyen Zadawa.

Kauyen na nan a yankin Hardawa da ke karamar hukumar Misau ta jihar Bauchi.

Jami'ai a karamar hukumar sun shiga rikicin wanda ya kai ga mutuwar wasu daga cikinsu a kauyen.

Gidan talabijin na Channels ya gano cewa, rikicin ya barke a ranar Litinin inda ya kai har safiyar Talata yayin da wasu fusatattun mutane suka dauka fansa.

A yayin da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Ahmad Wakili, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Ya ce tuni aka tura jami'an tsaro yankin kuma komai ya daidaita tare da dawowar zaman lafiya.

Amma kuma wasu daga cikin wadanda suka samu rauni an mika su asibitin gwamnatin tarayya da ke Azare inda suke karbar taimakon likitoci.

KU KARANTA: Harkallar diban aiki: 'Yan majalisa sun kori ministan Buhari bayan musayar yawu

A wani labari na daban, sautin fashewar wasu abubuwa masu girzgiza kasa a cikin dajin jihar Zamfara a sa'o'in farko na ranar Talata ya firgita manoma yayin da suke ayyuka a gonakinsu, jaridar Daily Trust ta gano.

Faseh-fashen wanda aka ji a wani daji kusa da yankin Rukudawa da ke da nisan kilomita 7 tsakaninsa da garin Zurmi na karamar hukumar Zurmi, ya matukar tada hankalin jama'a da yawa.

Wani mazaunin yankin mai suna Mustapha Saadu, ya ce wurin karfe 7 na safe ne suka fara jin fashewar abubuwan daga garin Zurmi. Kowanne sauti kuwa na hade da tsananin kara tare da girgizar kasa wanda ke barazanar yaye kwanon saman gidajen jama'a.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel