COVID-19: Sakataren gwamnatin jihar Osun ya harbu da korona

COVID-19: Sakataren gwamnatin jihar Osun ya harbu da korona

Wole Oyebamiji, sakataren gwamnatin jihar Osun ya kamu da cutar coronavirus. Kwamishinan lafiya na jihar, Rafiu Isamoto, ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Talata.

Jihar ta tabbatar da harbuwar karin mutum 10 da muguwar cutar bayan sallamar mutum daya da ya warke daga cutar korona.

Kamar yaadda kwamishinan ya bayyana, hauhawar yawan masu cutar a jihar ya biyo bayan halayyar mazauna jihar na take dokokin kariya daga muguwar cutar.

"Idan aka lura, yawan masu cutar ya fara hauhawa ne a makonni biyu da suka gabata. Dalilin kuwa a bayyane yake. Jama'armu na nuna halin ko in kula a kan cutar.

"Rashin kiyaye dokokin dakile yaduwar cutar na daya daga cikin dalilan da ke kawo yawaitar masu kamuwa. A halin yanzu muna zargin cutar na yaduwa tsakanin mutane," yace.

A cewarsa, "Gwamnati za ta sake duba al'amarin, za mu sanar da dokoki masu tsauri don kiyaye yaduwar cutar.

"A halin yanzu, ko kama mutum aka yi ana tilasta shi killace kansa a matsayin hanyar dakile yaduwar muguwar cutar.

COVID-19: Bayan harbuwar gwamnan APC, sakataren gwamnatinsa ya kamu da korona
COVID-19: Bayan harbuwar gwamnan APC, sakataren gwamnatinsa ya kamu da korona. Hoto daga The Cable
Asali: Twitter

KU KARANTA: Gwamnan Niger ya rage wa kansa da masu riƙe da muƙaman siyasa albashi

"Za mu kafa kotun tafi da gidanka da za ta fara ladabtar da masu karantsaye ga dokar hana yaduwar cutar. Dole ne mu hada kai da gwamnati wurin hana yaduwar cutar.

"Hakazalika, ina son sanar da ku cewa sakataren gwamnatin jihar da wasu ma'aikatan da ke tattare da shi sun kamu da cutar. Amma da sauki al'amarin don suna samun kulawar da ta dace."

Ya kara da cewa, a ranar 30 ga watan Yuni, akwai mutum 74 da suke dauke da cutar a jihar.

Amma kuma daga cikin mutum 127 da aka gano na dauke da cutar a jihar, 48 sun warke sarai yayin da mutum 5 suka riga mu gidan gaskiya.

A ranar Talata ne Gwamnan jihar Ondo ya sanar da kamuwarsa da cutar korona. Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata 3O ga watan Yuni ta wani faifan bidiyo da ya wallafa a sahihin shafinsa na Twitter.

Akeredolu ya ce a lokacin da ya samu sakamakon gwajin, baya da alamomin cutar kuma tuni ya killace kansa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel