Gwamnan Niger ya rage wa kansa da masu riƙe da muƙaman siyasa albashi

Gwamnan Niger ya rage wa kansa da masu riƙe da muƙaman siyasa albashi

Gwamnan jihar Niger Abubakar Sani Bello ya bayar da umurnin rage albashin dukkan masu riƙe da muƙaman siyasa a jiharsa da kashi 30 cikin 100.

Wadanda za a rage wa albashin da allawus sun hada da Gwamnan da mataimakinsa, Kwamishinoni, mashawarta na musamman da sauran musu muƙaman siyasa.

Ragin albashin da allawus ɗin zai fara aiki nan take kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Hakan na cikin wata sanarwa ce da sakataren gwamnatin jihar, SSG, Ahmed Ibrahim Matane ya fitar.

Gwamna Bello ya rage wa kansa da masu riƙe da muƙaman siyasa albashi
Gwamna Bello ya rage wa kansa da masu riƙe da muƙaman siyasa albashi
Asali: UGC

Sanarwar ta kuma ce ragin albashin na wuccin gadi ne saboda illar da annobar Covid-19 ta yi wa tattalin arzikin jihar.

DUBA WANNAN: Labari da ɗumi-dumi: Gwamna Akeredolu ya kamu da cutar korona

Gwamnatin za ta koma biyan albashi da allawus kamar yadda ta saba da zarar annobar ta wuce kuma tattalin arziki ya koma yadda ya ke.

"An yi ragin na wuccin gadi ne saboda hallin matsin tattalin arziki da annobar coronavirus ta jefa jihar ciki.

"Gwamnatin jihar za ta cigaba da biyan albashi da allawus kamar yadda aka saba a baya da zarar al'amura sun fara daidaita," a cewar sanarwar.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, kun ji matar wani soja, Mrs Victoria Idakpini da mijinta, Lance Corporal Martins Idakpani sun yi karar Rundunar Sojin Najeriya, Shugaban hafsin sojojin kasa da Attoney Janar na kasa saboda take hakkin bil adama.

An kama Mrs Idakpani ne a makon da ta gabata kwanaki kadan bayan kama mijinta, Martins Idakpani, saboda cin mutuncin Shugaban rundunar sojojin kasa, Lt Janar Tukur Buratai, da Shugaban hafsoshin tsaro, Gabriel Olonisakin cikin wani bidiyo da ya rika yawo a intanet.

A cikin bidiyon, sojan ya yi kira ga shugabanin sojojin da su yi murabus tunda sun gaza wurin yaki da ta'addanci.

Ya kuma zarge su da nuna halin ko in kula da a kan batun tsaro a kasar da kuma yadda yan taadda ke cin karensu ba babbaka a kasar.

Ma'auratan cikin wani takardar kara da wani Apeh Abuchi ya shigar a madadinsu, sun ce an hana su ganin lauya kuma ba a sanar da su laifin da suka aikata ba tun kama su a makon da ta gabata.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, Akinyodem wanda shine shugaba na kasa na kungiyar lauyoyi ta Revolutionary Lawyers’ Forum, ya bayyana cigaba da tsare ma'auratan a matsayin saba doka.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel