NURTW: Akwai yiwuwar muyi ƙarin kuɗin mota saboda COVID-19

NURTW: Akwai yiwuwar muyi ƙarin kuɗin mota saboda COVID-19

- Kungiyar ma'aikatan sufuri ta kasa (NURTW) ta tabbatar da cewa rashin tallafin gwamnati zai sa ta kara kudin mota

- Kungiyar ta mika godiyarta ga gwamnatin tarayya da ta dage dokar hana zirga-zirga tsakanin jihohin fadin kasar nan

- Amma kuma ta ce dokokin da gwamnatin tarayya ta saka mata na tazara tsakanin fasinjoji zai rage musu yawan kudin shiga

Kungiyar ma'aikatan sufuri ta kasa, (NURTW) ta ce akwai yuwuwar ta yi karin kudin mota saboda dokokin zirga-zirga tsakanin jihohi da gwamnatin tarayya ta fitar.

A ranar Litinin, gwamnatin tarayyar ta dage dokar hana zirga-zirga tsakanin jihohin kasar nan wanda zai fara daga 1 Yuli, jaridar The Cable ta wallafa.

Amma kuma gwamnatin tarayya ta wajabta duba dumin jikin fasinjoji tare da hana cunkoso a tashoshin mota.

Ana bukatar motocin da su rage fasinjoji zuwa kashi hamsin na yawan wadanda suke dauka a baya.

Kabiru Yau, mukaddashin sakataren NURTW, ya ce wannan umarnin ga masu ababen hawa zai rage kudin da ke shigowa direbobin.

Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta rage kudin da take cajar masu ababen hawa don saukaka musu.

NURTW: Akwai yiwuwar muyi ƙarin kuɗin mota saboda COVID-19
NURTW: Akwai yiwuwar muyi ƙarin kuɗin mota saboda COVID-19. Hoto daga The Cable
Asali: Twitter

KU KARANTA: Labari da ɗumi-ɗumi: Buhari ya naɗa sabon jami'i mai kare lafiyarsa

"Muna godiya ga gwamnatin tarayya da ta dage doka. Ci gaba ne babba saboda masu aikin sufurin sun kwashe watanni uku zaune a gida babu wani kudin da ke shigowa," yace.

“A kalla, mutanenmu za su fara aiki tare da samun abinda za su ciyar da iyalansu. Amma kuma a lokacin daya, tazarar da za a dinga badawa a baben hawa zai rage kudin da dirobin za su din samu.

“Muna kira ga gwamnati da ta bada tallafi don rage asarar da direbobin za su dinga yi ko kuma bamu da dabarar da ta wuce mu kara kudin mota.

"Hakan zai sa mu cike gurbin asarar kudin da za mu yi saboda yawan fasinjoji da aka rage. Idan ba a rage ba, ko kudin man fetur ba zai rufa ba.

“Idan hakan ta faru, wacce riba aka samu? Me za ka bai wa mai abun hawa? A don haka muke kira ga gwamnati da ta tallafa tare da dubawa," yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel