Labari da ɗumi-dumi: Gwamna Akeredolu ya kamu da cutar korona

Labari da ɗumi-dumi: Gwamna Akeredolu ya kamu da cutar korona

- Gwamna Rotimi Akeredolu ya harbu da kwayar cutar Covid-19

- Gwamnan na jihar Ondo ya sanar da hakan ne a ranar Talata ta shafinsa na Twitter

- Akeredolu ya bukaci mutanen jiharsa su kwantar da hankulansu kuma su taya shi da addu'a

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata 3O ga watan Yuni ta wani faifan bidiyo da ya wallafa a sahihin shafinsa na Twitter.

Akeredolu ya ce a lokacin da ya samu sakamakon gwajin, baya da alamomin cutar kuma tuni ya killace kansa.

Labari da ɗumi-dumi: Gwamna Akeredolu ya kamu da cutar korona
Labari da ɗumi-dumi: Gwamna Akeredolu ya kamu da cutar korona
Asali: Depositphotos

Ya bukaci mutanen jiharsa su taya shi da adduo'i inda ya ce, "a halin yanzu ina bukatar adduoin samun sauki daga gare ku."

A cikin faifan bidiyon, Akeredolu ya ce, "Kwanakin baya na kamu da zazabin cizon sauro kuma na warke. A lokacin da muka tafi taron NEC na jamiyyar mu ta APC, takwarori na sun janyo hankali na.

DUBA WANNAN: Labari da ɗumi-ɗumi: Buhari ya naɗa sabon jami'i mai kare lafiyarsa

"Na yi magana da daya daga cikinsu, ya jawo hankali na cewa bai dace a rika wasa da zazzabin cizon sauro ba a halin yanzu na annoba kuma ya ce in tafi in yi gwajin Covid-19.

"Sakamakon gwajin ya fito a ranar 3O ga watan Yunin 22. Sakamakon ya nuna na kamu da cutar. Amma jiki na lafiya kalau ba ni da alamomin cutar. Bana jin wani canji a jiki na. Likitoci na sun ce in fara shan magungunan cutar sannan in killace kai na."

Gwamnan ya tabbatar wa mutanen jihar Ondo cewa ayyukan gwamnatin jihar zai cigaba yadda aka saba kuma zai rika aiki a killace a gidansa.

Ya kara da cewa nan da wasu kwanakin za a sake yi masa gwajin domin duba ko ya warke ko kuma akasin hakan.

Akwai mutane 276 da suka kamu da coronavirus a jihar ta Ondo kamar yadda Hukumar Kiyayye Cututtuka Masu Yaduwa, NCDC ta sanar a ranar Litinin inda sabbin mutum 32 suka kamu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel