Yadda 'yan sanda suka damke budurwar da taje birne cikin da aka cire mata

Yadda 'yan sanda suka damke budurwar da taje birne cikin da aka cire mata

Rundunar 'yan sandan jihar Anambra ta tabbatar da damke wata budurwa mai shekaru 24 a yayin da take kan hanyar zuwa birne cikin da aka zubar mata.

Budurwar mai suna Chidera Nwaoga, an kama ta ne wurin karfe 9 na dare a kauyen Ofianta da ke Nsugbe a ranar 20 ga watan Yunin 2020, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Anambra, Haruna Mohammed, ya ce an damke wanda ya zubar da cikin, mamallakin wani dakin shan magani ne.

Ya bayyana cewa, "A ranar 20 ga watan yunin 2020 wurin karfe 9 na dare, jami'an 'yan sanda tare da hadin guiwar 'yan banga sun kama wata Chidera Nwaoga a kauyen Nsugbe mai shkaru 24.

"An kama 'yar asalin karamar hukumar Izzi ta jihar Ebonyi dauke da diya mace wacce bata gama girma ba a mahaifa cikin bokitin roba.

"Tana kan hanyar zuwa birne jaririyar ne a lokacin da aka damke ta.

"Binciken farko ya nuna cewa ta isa wurin wani mai dakin shan magani bayan da cikinta ya tsufa.

Yadda 'yan sanda suka damke budurwar da taje birne cikin da aka cire mata
Yadda 'yan sanda suka damke budurwar da taje birne cikin da aka cire mata. Hoto daga shafin Linda Ikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yanzu na fara lalata da mijinki: Karuwa ta yi wa matar aure 'zagin kare dangi' (Bidiyo)

"Odimegwu Ikunne mai shekaru 51 dan kauyen Nando ne amma yana zama a kauyen Akpalagu da ke Nsugbe, ya yi mata allura inda daga bisani ya burgo jaririyar."

Bayan wani bincike da aka yi a farfajiyar dakin shan maganin, an samo lalatattun magunguna tare da sirinji, takardar ta kara da cewa.

"Chidera wacce ta jigata sakamakon jini da ta rasa, an kamata amma a yanzu ta warke bayan kular masana kiwon lafiya da ta samu a asibitin Multicare 33.

"A halin yanzu, an birne gawar jinjirar bisa ga shawarar masana kiwon lafiya. Kwamishinan 'yan sandan jihar John B. Abang ya bada umarnin mika al'amarin gaban sashen binciken laifuka na musamman," ya ce.

A wani labari na daban, tsoho mai shekaru 71 da aka kama shi da laifin yi wa yarinya mai shekaru 13 fyade tare da amfani da ita wurin yin sata a jihar Gombe, ya bada labarinsa.

A yayin da aka tambayi Ashiru Sule a kan yadda abun ya faru, ya ce "yarinya ta sanar da cewa nayi mata fyade kuma na ce ta dinga sato min masara. Ni ina siyar da masara ne kuma ita ke kawo min."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel