Shugaban hukumar NIS ya garagadi ma su neman aiki, ya yi karin bayani a kan hanyar daukan aiki
Hukumar kula da shige da fice ta kasa (NIS) ta gargadi ma su neman aiki da ita a kan su gujewa fadawa hannun 'yan damfara da ke neman kudi a hannunsu da sunan za su sama mu su aiki a hukumar.
Shugaban hukumar NIS na kasa, Muhammad Babandede, ne ya bayar da wannan sanarwa a cikin wani jawabi da ya fitar ranar Talata a Abuja.
Babandede ya fitar da jawabin ne a matsayin martani a kan wani adireshin yanar gizo da ke yawo a dandalin sada zumunta da sunan na daukan aiki ne a hukumar NIS.
"Aiki ne na 'yan damfara da ke son cutar jama'a, su rabasu da 'yan kudinsu da su ka sha wahalar nema.

Asali: UGC
"Mun sha yin gargadi a baya kuma har yanzu ba zamu daina ba; jama'a su kauracewa duk wani sako ko sanarwar da ba a shafin yanar gizo da dandalin sada zumunta na hukumar NIS aka wallafa ba.
DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun kama 'yan bindigar da su ka kashe Dakta Audu bayan karbar N7.5m kudin fansa
"Ba a nema balle har a karbi kudin wani mai neman aiki da sunan za a taimake shi, ku gaggauta sanar da ofishin 'yan sanda ma fi kusa a duk lokacin da wani ma'aikacin hukumar NIS ko wani mutum ya nemi ku bashi kudi domin ya taimaka mu ku wajen samun aiki a NIS," a cewar Babandede.
Babandede ya kara da cewa hukumar NIS za ta yi amfani da sahihan jaridu da kafafen yada labarai domin isar da sako ga jama'a a kan hanyoyi da matakan samun aiki a hukumar idan bukatar hakan ta taso.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng