Jami'an tsaro sun amshi cin hancin N44bn yayin dokar kulle a fadin tarayya

Jami'an tsaro sun amshi cin hancin N44bn yayin dokar kulle a fadin tarayya

Wata kungiyar fafutuka mai suna International Society for Civil Liberties and Rule of Law (Intersociety), ta yi zargin cewa jami'an tsaron Najeriya da shugabanninsu sun samu makudan kudi lokacin dokar kulle, The Sun ta ruwaito.

Za ku tuna cewa gwamnatin tarayya da wasu gwamnonin jihohin Najeriya sun kafa dokar hana fita da sufuri don takaita yaduwar cutar Korona.

Binciken kungiyar Intersociety ya nuna cewa cikin watanni 3, tsakanin 30 ga Maris zuwa 30 ga Yuni, jami'an tsaro sun karbi akalla N44 billion matsayin cin hanci wajen mutane.

A takardar da kungiyar ta saki jiya a Onitsha kuma shugabanta, Emeka Umeagbalasi; da wasu suka rattafa hannu, sun ce bincikensu ya kasance ne kadai kan masu motoci a cikin gari da iyakokin Najeriya amma banda jiragen sama da na ruwa.

Jami'an tsaro sun amshi cin hancin N44bn yayin dokar kulle a fadin tarayya
Jami'an tsaro sun amshi cin hancin N44bn yayin dokar kulle a fadin tarayya
Asali: Twitter

Kungiyar ta ce jami'an tsaron da suka amsa wadannan makudan kudin na cin hanci sun hada da Sojoji, yan sanda, jami'an Road Safety, jami'an NSCDC (Sibil defense) da jami'an kwastam.

Hakazalika an samu jami'an Sojin sama da na ruwa da kashi a gindi musamman lokutan da aka sanyasu kan titi ko cikin rundunar kare iyakokin Najeriya don hana mutane shigowa kasar.

A lissafin da kungiyar tayi filla-filla an karbi cin hancin N8 billion a iyakokin Najeriya kuma sun karbi N2.7 billion a kan titunan cikin gari.

A yanki-yanki, sun karbi N7.2bn a kudu maso yamma, N6.5 billion a Kudu maso mudu, N5.5 billion a kudu maso yamma, N4 billion a Arewa maso yamma, N3bn a Arewa ta tsakiya da kuma N3bn a Arewa maso yamma.

Bugu da kari, an karbi N4bn da sunan kudin beli bayan an kama mutane bisa zalunci.

Saboda haka, kungiyar ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta cire dokar hana sufuri tsakanin jihohin Najeriya saboda azurta jami'an tsaro kawai hakan ke yi.

Bayan sa'o'i, gwamnatin tarayya ta sanar da janye dokar hana sufuri tsakanin jihohi. kwamitin yaki da cutar Korona ta kasa PTF ta sanar da hakan yayin hira da manema labarai a Abuja ranar Litinin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel