Da dumi-dumi: Sabbin mutum 566 sun kamu da cutar korona a Najeriya

Da dumi-dumi: Sabbin mutum 566 sun kamu da cutar korona a Najeriya

Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta ce annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 566 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11.23 na daren ranar Litinin 29 ga Yunin shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa karin sabbin mutum 566 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka;

Da dumi-dumi: Sabbin mutum 566 sun kamu da cutar korona a Najeriya
Da dumi-dumi: Sabbin mutum 566 sun kamu da cutar korona a Najeriya
Asali: Twitter

Lagos-166

Oyo-66

Delta-53

Ebonyi-43

Plateau-34

Ondo-32

FCT-26

Ogun-25

Edo-24

Imo-15

Bayelsa-13

Benue-12

Gombe-11

DUBA WANNAN: Bidiyon wani mutum da mace suna lalata a kan titi cikin motar UN ya jawo cece-kuce

Kano-11

Kaduna-11

Osun-8

Nasarawa-7

Borno-5

Katsina-2

Anambra-2

Alkalluman da hukumar ta dakile cututtukan ta fitar a ranar Litinin 29 ga Yunin shekarar 2020 ya nuna cewa jimillar wadanda suka kamu da cutar ta korona a kasar 25,133.

An sallami mutum 94O2 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 573.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, kun ji cewa Allah ya yi wa babban alkalin jihar Kogi, Nasir Ajanah rasuwa.

Marigayin ya rasu ne a cibiyar killace masu jinyar cutar COVID-19 da ke Gwagwalada a Abuja kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Wani daga cikin iyalansa ya kuma tabbatar wa majiyar Legit.ng rasuwarsa a safiyar yau.

Daya daga cikin hadiman gwamna Yahaya Bello na jihar shima ya rasu a wani asibiti da ke Abuja a cikin kwanakin baya bayan nan.

Kwamishinan watsa labarai na jihar, Kingsley Fanwo bai amsa tambayar da aka masa ba a kan rasuwar amma sakataren watsa labaran gwamnan, Mohammed Onogwu ya sada majiyar Legit.ng da iyalan Ajanah.

Ya ce, "Sune za su fara bayar da sanarwa game da rasuwar."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel