Da duminsa: Buratai ya koma Katsina, garinsu shugaba Buhari

Da duminsa: Buratai ya koma Katsina, garinsu shugaba Buhari

- Shugaban rundunar sojin Najeriya, Laftanal janar Tukur Yusuf Buratai ya ce ya koma jihar Katsina

- A watanni kalilan da suka gabata, 'yan bindiga sun saka jihar gaba inda suka gallabesu da hare-hare

- Buratai ya ce yana jihar ne don tsara yadda al'amuran sabbin atisayen da aka kaddamar don su wanke jihar daga sharrin 'yan bindiga

Shugaban rundunar sojin Najeriya, Laftanal janar Tukur Yusuf Buratai, a ranar Litinin, 29 ga watan Yuni ya sanar da komawarsa kacokan zuwa jihar Katsina bayan tsanantar hare-haren 'yan bindiga a jihar.

Buratai ya sauka a jihar ne don tsara yadda al'amuran sabon atisayen da suka kaddamar, wanda aka shiryasa don kakkabe 'yan bindiga daga yankin arewa maso yamma zai kasance.

"Na iso ne tun kwanaki biyu da suka gabata kuma zan kwashi wani lokaci don shirya ayyukan dakarunmu da kuma yadda za mu shawo kan wasu kalubale da suka addabemu," Buratai ya sanar da gwamna Aminu Masari bayan ziyarar da ya kai masa.

Ya kara da cewa: "Mun san yadda tsaron yankin arewa maso yamma ya tagayyara wanda a halin yanzu ya zama abun daga hankali.

"Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin fitar da tsari ko matakai masu kyau daga cibiyoyin tsaro.

"Daga cikin kokarinmu na ganin mun bi umarnin shugaban kasa na samar da tsaro mai daidaituwa, rundunar sojin Najeriya ta hada ayyukanta da sauran cibiyoyin tsaro a nan yankin arewa maso yamma."

Da duminsa: Buratai ya koma Katsina, garinsu shugaba Buhari
Da duminsa: Buratai ya koma Katsina, garinsu shugaba Buhari. Hoto daga NA
Asali: Facebook

KU KARANTA: Akwai yuwuwar FG ta rufe kananan hukumomi 18 a Najeriya (Sunaye)

A martanin Gwamna Aminu Masari, ya jajanta yadda 'yan bindiga ke cin karensu babu babbaka a sassan jihar. Hakan yasa wasu sassan jihar aka kasa shugabantarsu.

Kamar yadda gwamnan yace, jihar tana fuskanci miyagun ayyukan 'yan bindigar wanda hakan yasa jama'a ke tserewa gudun hijira.

A kalamansa: "Abinda mutanen nan suka sani shine karfi kuma har sai mun fi karfinsu, sannan ne za mu iya shawo kan matasalar da ta addabemu.

"A don haka ina kira ga cibiyoyin tsaro da su gane cewa 'yan bindigar nan ba su fahimtar wani yare da ya wuce ruwan wuta."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel