Labari da ɗumi-ɗumi: Buhari ya naɗa sabon jami'i mai kare lafiyarsa

Labari da ɗumi-ɗumi: Buhari ya naɗa sabon jami'i mai kare lafiyarsa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin mataimakin kwamishinan 'yan sanda, Aliyu Musa a matsayin babban jami'i mai tsaron lafiyarsa.

Kakakin shugaban kasa, Garba Shehu ne ya bayyana hakan cikin wani sanarwar da ya wallafa a shafinsa na Twiter a ranar Litinin.

A cewar sanarwar, Musa dan asalin jihar Niger ne kuma kafin nadinsa ya yi aiki ne a Zone 5 na Benin City.

Shehu ya rubuta cewa, "an nada Musa ne bayan an yi wa magabacinsa, Kwamishinan 'Yan sanda, Abdulkarim Dauda sauyin wurin aiki."

DUBA WANNAN: Bidiyon wani mutum da mace suna lalata a kan titi cikin motar UN ya jawo cece-kuce

Dauda yana daya daga cikin jami'an tsaron da aka yi wa canjin wurin aiki bayan harbe-harben da aka yi a fadar shugaban kasa da ya shafi masu tsaron Aisha Buhari.

A wani labarin daban babban mai bai wa shugaban kasa shawara a kan yada labarai, Garba Shehu, ya ce Shugaba Muhammadu Buhari da jigon jam'iyyar APC, Bola Tinubu, na nan tare.

Fadar shugaban kasa ta yi kira ga masu hasashe da su dakata da yada labarai marasa tushe, jaridar The Punch ta ruwaito.

Shehu ya sanar da hakan ne a wata takardar da ya fitar yayin martani ga rahotannin da suka shafi sauke 'yan kwamitin gudanar da ayyuka na jam'iyyar da shugaban kasar yayi.

Ya rubuta, "Domin bada bayani kai tsaye, wajen kafa jam'iyyarmu mai daraja da bada shugabancinta, shugaban kasa Muhammadu Buhari da Bola Tinubu ne a kan gaba.

"Sun kasance masu tabbatar da tsarin damokaradiyya tare da bukatar 'yan kasa ba siyasar bangare ba.

"Har a yanzu suna tare da juna. Dangantakarsu na nan da karfi kamar yadda take a da. Su kadai suka san yadda suka gina dangatakarsu tare da kiyayeta."

Mai magana da yawun shugaban kasar ya ce amfanin amsa bukatar da kwamitin shugabannin jam'iyyar APC suka mika wa Buhari, shine janye rikicin cikin gidan da ya addabi jam'iyyar.

Shehu ya ce jam'iyyun adawa na yin amfani da duk wata dabararsu da kuma magoya bayansu a kafafen sada zumuntar zamani don shiga tsakanin shugabannin biyu amma sun kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel