Yanzu na fara lalata da mijinki: Karuwa ta yi wa matar aure 'zagin kare dangi' (Bidiyo)

Yanzu na fara lalata da mijinki: Karuwa ta yi wa matar aure 'zagin kare dangi' (Bidiyo)

- Bidiyon wata karuwa na yi wa matar aure zagin kare dangi ya janyo cece-kuce a kafar sada zumuntar zamani

- A bidiyon, an ga karuwar na bankawa matar auren zagi tare da ilimantar da ita yadda ake gamsar da namiji a gado

- Ta kara da yin alkawarin cewa ba za ta taba barin mijin ba duk da sanin da tayi yana da mata

Bidiyon wata karuwa da ke zagin matar aure ya shiga shafukan sada zumuntar zamani kuma ya janyo cece-kuce, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

A bidiyon mai tsawon dakika 44, an ji karuwar wacce 'yar asalin jihar Delta ce ta kira matar auren a waya inda take ta kunduma mata zagi.

A bidiyon an ji tana 'ilimantar' da matar auren a kan yadda za su gamsar da mazansu a gado.

Ta kara da yin alkawarin cewa ba za ta bar mijin matar da ta gama zagi ba har abada.

KU KARANTA: Kasuwanci muka yi da ita - Tsohon da ya yi wa yarinya mai shekaru 13 fyade

A wani labari na daban, wasu da ake zargin 'yan kungiyar asiri ne sun sace wata budurwa mai suna Patience Emmanuel mai shekaru 20 da ke karatu a jami'ar jihar Bauchi.

Bayan nan, sun sanar da mahaifinta cewa basu bukatar kudi, budurcinta kadai suke bukata.

A yayin bayyanawa manema labarai halin da yake ciki, Emmanuel Kushi, wanda ma'aikacin gwamnati ne, ya sanar da cewa diyarsa ta je gidan dan uwanta da ke Rafin Zurfi a ranar Laraba, 24 ga watan Yuni da niyyar dauko wani abu.

Amma kuma bata isa gidan ba kuma ba a samunta ko a waya, shafin Linda Ikeji ya ruwaito. Zuwa da yamma, dan uwanta ya dinga kiranta amma ba a dauka.

Daga bisani kuwa ba a samun wayar kwata-kwata. Kushi ya bayyana cewa, "washegari na tura sakon karta kwana zuwa wayar diyata amma amsar da na samu ta bani mamaki."

"Kana tunanin za ka sake ganinta ne nan gaba? Wawa," aka bada amsa.

Kushi ya ce ya tafi gonarsa inda ya sake samun sako daga wadanda suka sace diyarsa. "Baba, diyarka na tare da mu. Bamu bukatar kudi, budurcinta kawai muke bukata. Kada ka nemeta."

Rikitaccen mahaifin ya ce yana kokarin gane sakon da aka turo masa amma sam bai yarda da ikirarinsu ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel