Kar a buɗe makarantu tukunna - ASUU ta gargadi gwamnati

Kar a buɗe makarantu tukunna - ASUU ta gargadi gwamnati

- ASUU ta gargadi gwamnatin tarayya a kan kada ta ba da umarnin buɗe makarantu a yanzu

- Shugaban ASUU, Biodun Ogunyemi, ya ce kada gwamnati ta kuskura ta cire dokar da ta shimfida kan makarantu saboda annobar korona

- Biodun ya ce mafi akasarin makarantu a fadin tarayya ba su da arzikin da za su iya cika sharuɗan da aka shata wanda sai an kiyaye kafin a buɗe makarantu

A yayin da ake ci gaba da kiraye-kiraye da yi wa gwamnatin tarayya matsin lamba, kungiyar malaman jami'o'in Najeriya ASUU, ta yi gargadi a kan buɗe makarantu a halin yanzu.

ASUU ta yi gargadin cewa, kada a kuskura a buɗe makarantu tukunna duba da yadda ake ci gaba da fama da annobar korona wadda ta hana ruwa gudu a kasar.

Furucin hakan ya fito ne daga bakin shugaban kungiyar ASUU na kasa, Farfesa Biodun Ogunyemi, yayin ganawa da manema labarai a ranar Litinin, 29 ga watan Yuni.

Ogunyemi ya sanar da cewa, ya kamata gwamnatin tarayya ta magance kalubalan da sashen ilimi ya ke fuskanta kafin ta yi la'akari da sake buɗe makarantu a fadin kasar.

Yayin da mahukuntan lafiya ke babatun yadda wasu ke kin kiyaye dokokin kare kai daga kamuwa da cutar, akwai bukatar gwamnati ta yi dogon nazari kafin ta yanke hukuncin buɗe makarantu.

Shugaban kungiyar ASUU na kasa, Biodun Ogunyemi
Hakkin mallakar hoto; Jaridar The Punch
Shugaban kungiyar ASUU na kasa, Biodun Ogunyemi Hakkin mallakar hoto; Jaridar The Punch
Asali: Twitter

Ya ce akwai bukatar gwamnati ta shige gaba wajen dabbaka matakai da cika ka'idodin da Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka a kasar NCDC ta shata kafin a buɗe makarantu da cibiyoyin ilimi.

Shugaban ASUU ya lissafa sharudan da NCDC ta shata da suka hadar da; samar da ababen wanke hannu na yau da kullum, takunkumin rufe fuska, wuraren killace masu cutar, da kuma sararin bayar da tazara.

Mista Ogunyemi ya ce shakka babu, mafi akasarin makarantu a fadin tarayyar kasar nan ba su da karfin arzikin cika wannan sharuda da aka shata, yana mai cewa dole sai gwamnati ta agaza.

Ogunyemi, wanda ya nuna damuwarsa game da yadda makarantu da yawa ba za su iya samar da sunadarin wanke hannu ba (sanitizer), ya ce da yawa daga cikinsu ma ba su da ruwan sha ballantana kuma na wanke hannu.

KARANTA KUMA: Yaki da ta'addanci: Sarkin Daura ya yabawa dakarun sojin kasa da sauran hukumomin tsaro

Ya kara da cewa, makarantu da dama ba su da wadataccen filin da za su dabbaka dokar nesa-nesa da juna da bayar da tazara.

Shugaban na ASUU ya ce, cika wannan sharuda da aka shata za su bukaci a batar da miliyoyin nairori, wanda kuma galibin makarantu ba su da hali.

Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta samar da kudaden gudanarwa ga shugabannin makarantu domin su iya cika wasu daga cikin sharudan da aka shata a makarantunsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel