Har mutane miliyan 1 sun nemi aikin N-Power a cikin sa'a 48 - Minista

Har mutane miliyan 1 sun nemi aikin N-Power a cikin sa'a 48 - Minista

A jiya Lahadi, 28 ga watan Yuni, gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana inda aka kwana a game da batun tsarin aikin N-Power, inda za a dauki sababbin Zubin matasa a fadin kasar.

Gwamnatin Najeriya ta ce kawo yanzu mutane fiye da miliyan guda sun nuna sha’awar samun wannan aiki. Hakan na zuwa ne bayan rade-radin cewa an yi wa shafin aikin kutse.

Ministar bada agaji da tallafin gaggawa da walwala ta kasa, ta ce sam ba a kai wa shafin hari ba.

Hajiya Sadiya Umar Farouq ta bayyana wannan ne a jiya da dare ta bakin mataimakiyar darektar harkokin yada labarai ta ma’aikatar, Rhoda Iliya.

A jawabin, ma’aikatar, an bayyana cewa: “Mun samu takardun mutane fiye da 1, 000, 000 daga fadin kasar nan a cikin kasa da sa’o’i 48 bayan mai girma minista Sadiya Umar Farouq ta bude sashen aikin N-Power a shafin ma’aikatar.”

“Shafin (N-Power) ya na samun mutum 100 masu rajista a cikin kowace dakika. Kuma zuwa karfe 7:38 (ranar Lahadi), mun samu mutane 1,001,045.”

KU KARANTA: Yadda za ka samu labarai a Facebook daga Legit Hausa

Har mutane miliyan 1 sun nemi aikin N-Power a cikin sa'a 48 - Minista
Minista Sadiya Farouk da Maryam Uwais
Asali: Facebook

Hakan ya na nufin a kusan mutane 6, 000 su ke rububin wannan aiki a cikin kowane minti guda, hakan ya na nufin a kowace sa’a, matasa 360, 000 su ke cike sunayensu a shafin neman aikin.

“Ma’aikatar ta na sake kara jaddadawa matasan Najeriya masu shekaru 18 zuwa 35 masu ilmi da marasa ilmi cewa za su iya neman aiki a wannan shiri wanda zai maida hankali a kan harkar noma.”

“An bude shafin ne ga duka ‘yan Najeriya wadanda su ka cike sharudan aikin.” Ma’aikatar ta yi alkawarin cewa za ayi adalci wurin daukar wadanda za su yi wannan aiki.

Jawabin ya kara da cewa: “Yawan wadanda su ka nemi wannan aiki ya nuna yadda matasan mu su ke bukatar abin yi, kuma su ka yarda da wannan tsari.”

Mai girma Hajiya Sadiya Umar Farouq ta tabbatar da wadannan alkaluma a shafinta na Twitter.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel