Yanzu-yanzu: Sabbin mutum 490 sun kamu da cutar Korona a Najeriya
Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta ce annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 490 a fadin Najeriya.
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11.28 na daren ranar Lahadi 28 ga Yunin shekarar 2020.
A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa karin sabbin mutum 490 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka;

Asali: Twitter
Lagos-118
Delta-84
Ebonyi-68
FCT-56
Plateau-39
Edo-29
Katsina-21
Imo-13
Ondo-12
Adamawa-11
DUBA WANNAN: Bidiyon wani mutum da mace suna lalata a kan titi cikin motar UN ya jawo cece-kuce
Osun-8
Ogun-8
Rivers-6
Kano-5
Enugu-3
Bauchi-3
Akwa Ibom-3
Kogi-1
Oyo-1
Bayelsa-1
Alkalluman da hukumar ta dakile cututtukan ta fitar a ranar Lahadi 28 ga Yunin shekarar 2020 ya nuna cewa jimillar wadanda suka kamu da cutar ta korona a kasar 25,567.
An sallami mutum 9007 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 565.
A wani labarin, kun ji cewa an birne gawar tsohon gwamnan jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi a ranar Lahadi a garin Ibadan babban birnin jihar Oyo.
An yi wa Ajimobi jana'iza irin ta koyarwar addinin musulunci sannan aka birne shi a gidansa da ke 6th Avenue, Yemoja Street, Oluyole Estate, Ibadan cikin yanayi na tsaro kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Gwamnatin jihar ta Oyo ta ki amincewa a birne marigayin a gidansa da ke Agodi GRA saboda ana shariar a kotu game da gidan duk da cewa nan iyalansa suka fi so.
An birne tsohon shugaban riko na jami'yyar All Progressives Congress, APC, mai mulki misalin karfe 10:05 na safe.
Ajimobi, mai shekaru 7 a duniya ya rasu ne a wani asibiti da ke Legas.
Rahotanni sun ce an bi dukkan dokokin birne wadanda suka mutu sakamakon cutar coronavirus yayin janai'zarsa.
Mutanen da suka hallarci jana'izar ba su kai 2 ba cikinsu har da matar tsohon gwamnan, Cif Florence Ajimobi da wasu daga cikin iyalansa na yan uwansa na kusa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng