Sarkin Bachama ya riga mu gidan gaskiya

Sarkin Bachama ya riga mu gidan gaskiya

Mun samu rahoton cewa, Hama Bachama kuma Sarkin Kabilar Bachama a jihar Adamawa, Mista Honest Stephen, ya riga mu gidan gaskiya.

Mista Timawus Mathias, mai rike da rawanin Nzobyalya a Hama Bachama kuma kakakin masarautar Bachama, shi ne ya ba da tabbacin wannan rahoto a ranar Lahadi cikin garin Numan.

Mathias ya ce Mai martaba Stephen ya yi kicibus da ajali da safiyar ranar Lahadi a fadarsa da ke garin Numan na jihar Adamawa.

Ya ce ya mutu ne bayan fama da wata 'yar takaitacciyar rashin lafiya. Kuma an fara shirye-shiryen gudanar da jana'izarsa bisa tanadin al'adun kabilar Bachama a Lamurde.

Homun Honest Irmiya Stephen, ya mutu yana da shekaru 66 a duniya, inji Mathias.

Atiku tare da Hama Bachama yayin da ya kai wata ziyara fadarsa
Atiku tare da Hama Bachama yayin da ya kai wata ziyara fadarsa
Asali: Twitter

An yi bikin nadin sauratar marigayi Stephen a ranar 15 ga watan Dasumban 2013, yayin da tsohon gwamnan jihar, Murtala Nyako, ya ba shi sandar girma.

Mathias ya kuma ba da tabbacin cewa, marigayin tsohon ma'aikacin sojin kasan Najeriya ne, wanda ya yi ritaya daga aikin domin karbar sarautar da ya gada a shekarar 2012.

Hama Bachama shi ne sarki na 28 a tarihin masarautar Bachama kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

An haifi marigayi Honest Irmiya a ranar 6 ga watan Maris na shekarar 1954 a jihar Legas.

Mahaifinsa Irmiya Stephen, yarima ne Masarautar Numupo yayin da kuma mahaifiyarsa, Lekoni Irmiya, ta kasance gimbiya a masarautar Kowo, wanda dukkaninsu ke karkashin masarautar Bachama.

KARANTA KUMA: Abiola Ajimobi: Ganduje da iyalinsa sun je ta'aziyya wurin sirikansu

Legit.ng ta ruwaito cewa, an binne gawar tsohon gwamnan jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi a ranar Lahadi a garin Ibadan babban birnin jihar Oyo.

An yi wa Ajimobi jana'iza irin ta koyarwar addinin musulunci sannan aka binne shi a gidansa da ke yankin 6th Avenue na layin Yemoja a unguwar Oluyole da ke birnin Ibadan cikin yanayi na tsaro.

Gwamnatin jihar ta Oyo ta ki amincewa a binne marigayin a gidansa da ke Agodi GRA saboda ana shari'a a kotu game da mallakar gidan duk da cewa nan iyalansa suka fi so.

An binne tsohon shugaban riko na jami'yyar APC tun da misalin karfe 10:05 na safe.

Ajimobi, mai shekaru 71 a duniya ya rasu ne a wani asibiti da ke Legas.

Rahotanni sun ce an bi dukkan dokokin birne wadanda suka mutu sakamakon cutar coronavirus yayin jana'izarsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel