Babban alkalin jihar Kogi, Nasir Ajanah ya rasu a cibiyar killace masu COVID-19
Allah ya yi wa babban alkalin jihar Kogi, Nasir Ajanah rasuwa.
Marigayin ya rasu ne a cibiyar killace masu jinyar cutar COVID-19 da ke Gwagwalada a Abuja kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Wani daga cikin iyalansa ya kuma tabbatar wa majiyar Legit.ng rasuwarsa a safiyar yau.
Daya daga cikin hadiman gwamna Yahaya Bello na jihar shima ya rasu a wani asibiti da ke Abuja a cikin kwanakin baya bayan nan.
Kwamishinan watsa labarai na jihar, Kingsley Fanwo bai amsa tambayar da aka masa ba a kan rasuwar amma sakataren watsa labaran gwamnan, Mohammed Onogwu ya sada majiyar Legit.ng da iyalan Ajanah.
DUBA WANNAN: Bidiyon wani mutum da mace suna lalata a kan titi cikin motar UN ya jawo cece-kuce
Ya ce, "Sune za su fara bayar da sanarwa game da rasuwar."
Duk da cewa Hukumar Kiyayye Cututtuka Masu Yaduwa, NCDC, kawo yanzu ta sanar da cewa mutum uku ne aka gano suna dauke da cutar a jihar, gwamnatin jihar ta cigaba da cewa babu cutar a jihar.
Ta zargi hukumar ta NCDC da yi wa jihar kage game da bullar cutar a jihar.
An haifi Ajanah ne a shekarar 1956 a karamar hukumar Okene, sunan mahaifinsa MJ Fari Ajanah.
Ya yi karatun lauya a Jamiar Ahmadu Bello ta Zaria kuma daga bisani ya zama cikaken lauya a kotun koli.
Daga bisani, Ajanah ya bude kamfaninsa na lauyoyi mai suna Nasiru Ajanah & Co a garin Okene inda ya yi aiki daga 1985 zuwa 1989.
Ya yi aiki daban daban da suka hada da shugaban kotun rikicin Kabba a Kogi a shekarar 1994; Shugaban kotun sauraron kararrakin zabe na jihar Adamawa a 1998; Mamba a Cibiyar zurfafa karatun Sharia (1999 and 2006) da shugaban kwamitin binciken gobarar filin tashin jirage na Murtala Mohammed a 2000.
Har wa yau, ya yi aiki a matsayin shugaban kotun sauraron karar zabe a jihar Akwa Ibom a 2007 sai kuma shugaban kotun sauraron karar zabe na jihar Rivers a 2008.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng