Hotunan yadda aka binne gawar Ajimobi a gidansa da ke Ibadan
An birne gawar tsohon gwamnan jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi a ranar Lahadi a garin Ibadan babban birnin jihar Oyo.
An yi wa Ajimobi jana'iza irin ta koyarwar addinin musulunci sannan aka birne shi a gidansa da ke 6th Avenue, Yemoja Street, Oluyole Estate, Ibadan cikin yanayi na tsaro kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Gwamnatin jihar ta Oyo ta ki amincewa a birne marigayin a gidansa da ke Agodi GRA saboda ana shariar a kotu game da gidan duk da cewa nan iyalansa suka fi so.

Asali: UGC

Asali: UGC
DUBA WANNAN: Bidiyon lalata: UN ta fara bincike a kan wandanda suka yi latata a motarta
An birne tsohon shugaban riko na jami'yyar All Progressives Congress, APC, mai mulki misalin karfe 10:05 na safe.
Ajimobi, mai shekaru 7 a duniya ya rasu ne a wani asibiti da ke Legas.

Asali: UGC

Asali: UGC
Rahotanni sun ce an bi dukkan dokokin birne wadanda suka mutu sakamakon cutar coronavirus yayin janai'zarsa.
Mutanen da suka hallarci jana'izar ba su kai 2 ba cikinsu har da matar tsohon gwamnan, Cif Florence Ajimobi da wasu daga cikin iyalansa da yan uwansa na kusa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng