Da na sani da tuni na koma jam'iyyar PDP - Gwamna Godwin Obaseki

Da na sani da tuni na koma jam'iyyar PDP - Gwamna Godwin Obaseki

Gwamnan jihar Edo, Godwin Nosaghase Obaseki, ya bayyana cewa da ya sani da tun kafin yanzu ya sauya sheka jam'iyyar PDP maimakon zaman azabar da yayi a jam'iyyar APC.

Ya ce maimakon APC da ta ci mutuncinsa lokacin da yake fuskantar kalubale, PDP ta nuna masa kula da soyayya.

Ya bayyana hakan ne a yau Asabar yayinda ya ke karbar takardar shaidar nasara a zaben fidda gwanin jam'iyyar tare da mataimakinsa, Philip Shaibu.

Obaseki yace: "Sai da muka shigo gidan nan (PDP) muka gano ashe nan ya kamata ace mun kasance tun farko."

"Ni da mataimaki na muna matukar godiya ga wannan babbar jam'iyyar. Kuma kamar yadda nace, mutum bai sanin abinda Allah ya tanadar masa."

"A lokacin da muke cikin halin kunci, lokacin da aka koremu cikin ruwa daga jam'iyyarmu, kun zo mana da babbar lemarku kuma kuka lullubemu."

Da na sani da tuni na koma jam'iyyar PDP - Gwamna Godwin Obaseki
Da na sani da tuni na koma jam'iyyar PDP - Gwamna Godwin Obaseki
Asali: UGC

KU KARANTA: Yan bindiga sun sake kai farmaki jihar Zamfara, sun kashe mutane 12

A bangare guda kuwa, Gwamnan Godwin Nosaghase Obaseki, ya yi ikirarin cewa lallai zai zarce kan kujerarsa na gwamna na karin shekaru hudu.

Obaseki ya bayyana hakan da safiyar Juma'a, 26 ga Yuni yayinda ya ke godiya bayan an alantashi matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwanin jam'iyyar People’s Democratic Party PDP a taron gangamin da ya gudana a Benin, babbar birnin jihar.

Ya siffanta nasararsa matsayin wanda zai wakilci jam'iyyar a zaben gwamnan 19 ga Satumba matsayin babbar nasara kan makiya dake kokarin kwace dukiyar jihar don cin gashin kansu.

Yace: "A yau, an kafa tarihi a Najeriya, saboda nasarar da muke murna yau wata sufuri ce zuwa yanci na siyasa. Idan Allah ya yarda zan sake zama gwamna na karin shekaru hudu."

Obaseki ya jinjinawa sauran yan takaran, shugabannin jam'iyyar PDP, gwamnonin jam'iyyar da magoya bayansu da suka "sanyashi karkashin lemarsu lokacin da APC ta sharoshi cikin ruwa."

Yayin sanar da nasararsa, shugaban kwamitin zaben fidda gwanin kuma gwamnan jihar Bauchi, Bala Kauran Bauchi, ya ce Obaseki ya samu kuri'u 1,952.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel