Yan bindiga sun sake kai farmaki jihar Zamfara, sun kashe mutane 12

Yan bindiga sun sake kai farmaki jihar Zamfara, sun kashe mutane 12

Yan bindiga sun sake hallaka akalla mutane 12 a kauyen Unguwar Yabo, dake karamar hukumar Tsafe dake jihar Zamfara, The Punch ta ruwaito.

Wani mazaunin garin, Malam Sani Mohammad, ya bayyanawa manema labarai cewa yan bindigan sun shigo cikin garin kan babura kuma suka fara harbin kan mai uwa da wabi.

Malam Sani ya ce sai da suka kwashe sa'o'i a kauyen suna harbi kuma suna kwashe dukiyoyin mutane.

Bayan adadin mutanen da aka kashe, Mohammad ya ce da dama sun jikkata sakamakon harbi.

Ya ce babban yayansa, Ibrahim, na daya daga cikin wadanda aka kashe.

"Mun ga fitina. Wadannan mutanen marasa imani sun lalata kauyen saboda yawancin wadanda aka kashe ko ji wa rauni mutanen kirki ne da muke alfahari da su." A cewarsa

Ya ce da kyar ya tsallake rijiya da baya inda ya arce cikin daji.

KU KARANTA: Manyan Malamai sun halarci taron daurin auren 'dan marigayi Sheikh Ja'afar

Yan bindiga sun sake kai farmaki jihar Zamfara, sun kashe mutane 12
Yan bindiga sun sake kai farmaki jihar Zamfara, sun kashe mutane 12
Asali: Twitter

Kakakin hukumar yan sandan jihar, SP Mohammed Shehu, wanda ya tabbatar da labarin ya ce mutane hudu kadai aka kashe.

Ya kara da cewa wadanda suka jikkata kuwa an garzaya da su Asibitin Tsafe.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel