Babu abin sha'awa a APC - Gwamnonin PDP sun yiwa Yahaya Bello raddi

Babu abin sha'awa a APC - Gwamnonin PDP sun yiwa Yahaya Bello raddi

- Gwamnonin PDP sun karyata rahoton cewa wasu 10 cikinsu na shirin komawa APC

- Dirakta janar na kungiyar gwamnonin ya ce babu abin sha'awa a APC da zai sa wani a shigeta

- Sun gargadi gwamnan APC, Yahaya Bello, ya mayar da hankali wajen ganin cigaban al'ummarsa

Kungiyar gwamnonin People's Democratic Party PDP ta ce babu abin sha'awa a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da zai sa su sauya sheka.

Kungiyar karkashin jagorancin gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ta bayyana hakane yayin martani ga jawabin da gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, da yayi ranar Juma'a.

Yahaya Bello ya ce kimanin gwamnonin PDP 10 na shirin sauya sheka APC.

Babu abin sha'awa a APC - Gwamnonin PDP sun yiwa Yahaya Bello raddi
Babu abin sha'awa a APC - Gwamnonin PDP sun yiwa Yahaya Bello raddi
Asali: Facebook

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Na dau kaddarar abinda ya faru da ni, na hakura - Adams Oshiomole

Dirakta Janar da kungiyar gwamnonin PDP, C.I.D Maduabum, ya ce jawabin Yahaya Bello bai cancanci martani ba amma kawai za'ayi ne kawai saboda kada mambobin PDP su dauka gaskiya ne.

Yace: "Ya bayyana karara cewa wannan wani yunkuri ne da dauke hankulan mutane da kuma karawa mambobin APC karfin gwiwa bayan sun yi rashin gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, sakamakon rikicin da ya kunno kai cikin jam'iyyar."

"Gwamnonin PDP na mayar da hankali wajen yiwa jihohinsu aiki, baiwa al'ummarsu romon demokradiyya da kuma karfafa jam'iyyar."

"Babu wani abin sha'awa ko kadan da wani dan PDP zai gani, ballantana gwamna da zai sa shi sauya sheka APC. Jam'iyyar da ke fama da rikice-rikice da ko wani zababben shugaba bata da shi."

"Muna shawartan gwamna Yahaya Bello, ya mayar da hankali wajen baiwa al'ummar jihar Kogi mulki na kwarai."

Legit Hausa ta kawo muku rahoton cewa Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, ya ce kimanin gwamnonin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) 10 na hanyar sauya sheka All Progressives Congress (APC).

Ya bayyana hakan ne a hirar da yayi a shirin Politics Today na tashar Channels da yammacin Juma'a.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel