Kada ku birneshi a Masallaci - Yan Najeriya sun yi gargadi kan shirin birne Surukin Ganduje, Abiola Ajimobi

Kada ku birneshi a Masallaci - Yan Najeriya sun yi gargadi kan shirin birne Surukin Ganduje, Abiola Ajimobi

- Al'ummar Musulman Najeriya sun gargadi iyalan tsohon gwamnan Oyo, Isiaka Ajimobi

-Ajimobi ya mutu ranar Alhamis, 25 ga Yuni a asibitin First Cardiologist dake Legas sakamkon cutar Korona

- Mai magana da yawunsa, Bolaji Tunji, ya bayyana cewa za'a birneshi ranar Lahadi a cikin Masallaci

Biyo bayan sanarwan da iyalan surukin Ganduje, margayi Abiola Ajimobi, suka yi na cewa za a yi jana'izar mamaci ranar Lahadi, 28 ga Yuni, wasu Musulamai a Najeriya sun yi tsokaci.

A ranar Juma'a, mai magana da yawun gwamnan, Bolaji Tunji, ya ce za'a birne maigidansa a Masallacinsa dake Oke-Ado, birnin Ibadan misalin 12 na rana.

Wakilin Legit, Ibrahim Akinola, ya tattaro cewa Musulami a fadin Najeriya sun ce abinda iyalan marigayin ke kokarin yi na birneshi cikin Masallaci Haramun ne kuma hakan zai sa mutane su daina Sallah a Masallacin.

Kada ku birneshi a Masallaci - Yan Najeriya sun yi gargadi kan shirin birne Surukin Ganduje, Abiola Ajimobi
Surukin Ganduje, Abiola Ajimobi
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Na dau kaddarar abinda ya faru da ni, na hakura - Adams Oshiomole

Wani Malamin addini, Ustadh Ibrahim Tijjani, ya ce Manzon Allah (SAW) ya haramta birne Musulmai cikin Masallaci kamar yadda ya hana ginin Masallaci kan kaburbura.

Yace: "Manzon Allah (SAW) ya hana birne mutane cikin Masallaci da kuma gini kan kabari, hakazalika ya la'anci masu yin haka."

"Manzon tsira ya cewa wannan dabi'ar Yahudu da Nasara ne kuma yana iya kaiwa ga shirka."

Wani Malamin addinin, Sheik Abdullah Qasim ya tofa albarkacin bakinsa inda ya ce muddin aka birneshi ciki toh an kori mutane daga Masallacin.

Yace: "Al'ummar Musulmin jihar Oyo su farka, kada ku birne Sanata Ajimobi a cikin Masallacin nan. Kada ku kori mutane daga Masallacin."

Surukin Ganduje, Ajimobi ya mutu ranar Alhamis, 25 ga Yuni a asibitin First Cardiologist dake Legas bayan fama da cutar Korona.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel