Yanzu-yanzu: Na dau kaddarar abinda ya faru da ni, na hakura - Adams Oshiomole

Yanzu-yanzu: Na dau kaddarar abinda ya faru da ni, na hakura - Adams Oshiomole

Tsohon shugaban uwar jam'iyyar All Progressives Congress APC, Adams Oshiomhole, ya amince da hukuncin da majalisar zartaswa NEC ya yanke na rusa kwamitin gudanarwar da ya jagoranta.

Jaridar Punch ta samu rahoton cewa tsohon gwamnan jihar Edon ya bayyana hakan ne a hira da manema labarai a birnin tarayya inda yace yana alfahari da irin nasarorin da ya samu a lokacinsa.

Oshiomole ya ce tun a farko shugaba Muhammadu Buhari ne ya bukaceshi ya mulki jam'iyyar domin kawo sauyi kuma tun da yanzu ya yanke shawarar cewa a rusa, wajibi ne yayi masa biyayya matsayin jagora a jam'iyyar.

Yace: "An shirya zaman majalisar NEC kuma a karshe, an rusa kwamitin gudanarwa kuma yanzu ba ni bane shugaba,"

"Cikin mutunci shugaban kasa ya gayyaceni ofishinsa a 2018, shekaru biyu kenan da suka shude."

"Shugaban kasa ya ce idan ban kawo kauyi jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ba, toh mu manta da nasara a 2019."

"Kuma na sani sarai kawo canji na tattare da kalubale da dama da kuma daukan wasu matakai masu wuya, amma na rayuwar ta rikici ce, na amince da hakan kuma na yi imani na yi iyakan kokari na,"

Yanzu-yanzu: Na dau kaddarar abinda ya faru da ni, na hakura - Adams Oshiomole
Yanzu-yanzu: Na dau kaddarar abinda ya faru da ni, na hakura - Adams Oshiomole
Asali: UGC

Legit ta kawo rahoton cewa yan kwamitin majalisar gudanarwar da aka rusa ranar Alhamis sun fasa zuwa kotu.

Tsohon Sakataran kwamitin shugabannin jam'iyyar, Malam Waziri Bulama, ya bayyana haka jiya inda yace sun yanke shawara kawai a zauna lafiya.

Ya ce zaben 2023 ne ya sabbaba rikicin jam'iyyar.

Bulama yace: "Bayan mun nemi shawari daga wajen manya da masu ruwa da tsaki, mun amince da shawarar rusa kwamitin NWC da kuma kafa sabuwar kwamitin rikon kwarya karkashin Gwamna Mai Mala Buni."

"Muna ganin girman shugaban kasa. Mu ba yan tawaye bane. Duk maganganun da mukayi na cikin kundin tsarin mulkin jam'iyyar."

"Yanzu mun ajiye duk wata maganar kundin mulki ko kotu saboda zaman lafiya ya wanzu cikin jam'iyyar. Muna ganin girman manya, mun kira ga masu ruwa da tsaki kada su sake tayar da hayaniya cikin jam'iyyar."

"Zamu baiwa kwamitin Buni hadin kai wajen shirya taron gangami cikin watani shida masu zuwa."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel