An kai wa Fulani hari a ruga, an kashe biyu an sace shanu 103

An kai wa Fulani hari a ruga, an kashe biyu an sace shanu 103

Wasu mutane dauke da makamai da ake kyautata zaton 'yan bindiga ne a ranar Alhamis sun kai hari rugar Fulani inda suka kashe makiyaya biyu kuma suka sace shanu 103.

Lamarin ya faru ne a kauyen Osuku da ke Koton-Karfe a jihar Kogi kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Basarake, Ohimegye na Igu -Kotonkarfe, Alh. Abdulrazak Isah Koto ya shaidawa majiyar Legit.ng a ranar Juma'a cewa ya samu wasu shugabanin Fulani sun kira shi misalin karfe 11.23 na daren ranar Alhamis sun ce 'yan bindiga sun kai musu hari a ruga.

An kai wa Fulani hari a ruga, an kashe biyu an sace shanu 103
An kai wa Fulani hari a ruga, an kashe biyu an sace shanu 103. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

DUBA WANNAN: An kama wani fasto da bindigu masu yawa

Ya ce nan take ya tattaro yan banga suka bi sahun yan bindigan inda suka kwato wasu daga cikin shanun da aka sace.

Ya bayyana bukatar da ke akwai na samar da sansanin sojoji a kan babban titin Abuja-Lokoja.

Babban mataimakin gwamnan jihar na musamman a kan harkokin tsaro, Abdulkarim Isah ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Ya ce ya tuntubi wata tawagar jamian tsaro domin su bi sahun yan bindigan su kwato shanun da aka sace.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, 'yan sandan birnin tarayya Abuja sun kama kasurgumin mai garkuwa da mutane, Bello Saleh na kauyen Dobi da ke karamar hukumar Gwagwalada da aka dade ana nema ruwa a jallo.

A sanarwar da kakakin rundunar, DSP Anjuguri Manzah ya fitar, ya ce an kama wanda ake zargin ne a mabuyarsa da ke kauyen Paiko Kore na karamar hukumar Gwagwalada.

DSP Manzah ya ce wanda ake zargin da 'yan tawagarsa sun harbe wani Ejike Idoko mazaunin kauyen Dobi har lahira a yayin da ya yi kokarin hana su tafiya da matarsa mai juna biyu.

Ya ce ana cigaba da kokarin ganin an kamo sauran 'yan tawagar na Saleh tare da kwato bindigun da ke hannunsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel