Bidiyon yadda soji suka yi wa 'yan ta'adda 'ruwan wuta' a Tongule da Bukar Meram

Bidiyon yadda soji suka yi wa 'yan ta'adda 'ruwan wuta' a Tongule da Bukar Meram

Dakarun rundunar sojin saman Najeriya, NAF, ta yi nasarar kashe 'yan kungiyar Boko Haram da dama a Tongule da Bukar Meram a jihar Borno.

Hakan na cikin wata sanarwa ne da kakakin rundunar sojin, Manjo Janar John Enenche, ya fitar a ranar Asabar 27 ga watan Yunin shekarar 22

A cewar sanarwar, rundunar sojin ta kai harin ne a ranar Alhamis 25 ga watan Yuni.

Ta ce ta kai harin ne bayan samun sahihan shaidun gani da ido daga na'urar leken asiri (ISR) wacce ta leko sansani biyu na 'yan ta'addan da alamun mutane a ciki.

Bayan tabbatar da shaidun ne sai rundunar soji ta aika da jirgin yaki mai karfin aman wuta zuwa sansanin domin kaddamar da hari a kan 'yan ta'addan da sansaninsu da sauran wuraren buyansu da boye makamai.

Bidiyon yadda soji suka yi wa 'yan ta'adda 'ruwan wuta' a Tongule da Bukar Meram
Bidiyon yadda soji suka yi wa 'yan ta'adda 'ruwan wuta' a Tongule da Bukar Meram. Hoto daga Channels TV
Asali: UGC

Enenche, ya ce wannan na cikin hare haren da Dakarun Sojin Saman na ATF suka rika kaiwa karkashin atisayen Operation Lafiya Dole da Operation Long Reach.

Ya cigaba da cewa, "A Tongule inda aka gano cewa yan Boko Haram suna taruwa, naurar leken asiri ta NAF ta gano a kalla yan taada 35 a wurare daban daban a sansanin yayin da za ta kai harin.

"Bama baman da jiragen yakin suka saki sun sauka a sansanin inda suka lalata gine-ginen da ke sansanin tare da kashe yan ta'addan masu yawa.

"Kazalika, an kai wani harin a wani cibiyar tsara zirga zirgan yan Boko Haram da ke Bukar Meram da ke kusa da tafkin Chadi inda aka kashe 'yan ta'adda da dama tare da lalata sansanin."

Ga bidiyon harin nan a kasa

KU KARANTA: Tallafin ruwan leda: Jama'a sun caccaki uwargidan gwamnan Bauchi

Shugaban hafsin sojojin saman Najeriya, Air Marshal Sadique Abubakar ya yaba wa kokarin Rundunar Dakarun Sojin saman bisa jajircewarsu da nuna kwarewa wurin aiki.

Wannan na zuwa ne a lokacin da Hedkwatan Tsaro ta kasa ta umurci sojojin su kara zage damtse wurin ganin sun kawo karshen barazanar 'yan ta'adda da sauran miyagu a kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel