Tsohon mataimakin shugaban Hukumar Kwastam, Olumudi ya rasu a Kogi

Tsohon mataimakin shugaban Hukumar Kwastam, Olumudi ya rasu a Kogi

Tsohon mataimakin shugaban hukumar hana fasa kwabri a Najeriya, Kwastam na kasa kuma jagoran alumma, Cif James Olumudi ya rasu.

Shugaban kwastam din ya rasu ne a garin Kabba a karamar hukumar Kabba-Bunu a jihar Kogi a ranar Jumaa.

Ya rasu yana da shekara 72 a duniya.

Daily Trust ta ruwaito cewa Cif Olumudi yana cikin koshin lafiya har zuwa safiyar ranar da ya rasu inda ya koka cewa cikinsa na ciwo.

Tsohon mataimakin shugaban Hukumar Kwastam, Olumudi ya rasu a Kogi
Tsohon mataimakin shugaban Hukumar Kwastam, Olumudi ya rasu a Kogi. Hoto daga Premium Times
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Tallafin ruwan leda: Jama'a sun caccaki uwargidan gwamnan Bauchi

Majiyar ta da ta tabbatar da rasuwarsa ta ce, "Eh, ya rasu. Ya biya maaikatan gidansa albashi da safe. Ya ci abincinsa sannan ya koka cewa cikinsa na ciwo kuma aka garzaya da shi asibitin St John inda ya rasu".

An haifi Olumudi a garin Kabba a ranar 28 ga watan Disambar 1948. Ya yi karatun frimari a St Mary Primary a Kaba da Baptist Day Primary School, Zaria daga shekarar 1953-1960.

Ya samu shiga Jamiar Ahmadu Bello University ta Zaria daga Satumban 1969 zuwa Yunin 1972 inda ya yi digiri a nazarin Tarihi.

A shekarar 1972 an dauki shi aiki a Hukumar Kwastam a matsayin Asst. Preventive Supt. kuma ya cigaba da aiki har ya kai matsayin mataimakin kwantrola Janar a shekarar 1999.

Rahotanni sun ce ya taka muhimmiyar rawa wurin kafa Hukumar Yaki da Miyagun Kwayoyi (NDLEA).

Olumudi ya yi murabus a shekara 2004 bayan ya yi aiki a jihohi da yawa da suka hada da Jos, Fatakwal, Ibadan, Legas, Kano da Sokoto.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel