An cire hotunan Adams Oshiomole daga sakatariyar APC
Kimanin kwana daya bayan fitittikar kwamitin gudanarwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), an tuge hotunan Adams Oshiomole daga allon gaban sakatariyar uwar jam'iyyar dake birnin tarayya Abuja.
Hakazalika hadimin daya daga cikin mambobin kwamitin Oshiomole ya fuskanci babban kalubale ranar Juma'a yayinda yake kokarin kwashe kayayyakin maigidansa daga ofishinsa.
Bayan rusa kwamitin gudanarwar da akayi ranar Alhamis, ma'aikatan sakatariyar suka yage dukkan hotunan Adams Oshiomole dake ofishoshinsu cikin farin ciki suna bayanin cewa mulkin kama karya yayi.
Yayinda aka tambayesu shin me yasa suke haka, daya daga cikin ma'aikatan yace: "Yanzu bashi da wani harka a nan. Ya yi kwantai. Ya tafi kawai, mun gaji da shi kuma bamu son ya sake dawowa nan."
"Yan shekarun da yayi a nan mun ji uwar bari."

Asali: Facebook
Legit Hausa ta kawo muku rahoton cew shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin shugaban kwamitin rikon kwaryar jam'iyyar All Progressives Congress APC da wasu gwamnoni a fadar Aso Villa yau Juma'a, 26 ga Yuni, 2020.
Gwamnonin wanda shahararrun masu adawa da tsohon shugaban APC Adams Oshiomole sun kai ziyarar domin yi ma Buhari godiya kan yadda ya shawo kan rikicin da ya kusa warware tsintsiyar jam'iyyar.
Daga cikin gwamnonin da suka kai ziyarar akwai gwamnan jihar Yobe kuma shugaban kwamitin rikon kwarya, Mai Mala Buni; da gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello.
Sauran sune gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello; da gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng