Da dumi-dumi: Karin mutum 684 sun kamu da coronavirus a Najeriya

Da dumi-dumi: Karin mutum 684 sun kamu da coronavirus a Najeriya

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa a Kasa (NCDC) ta ce annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 684 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 11.45 na daren ranar Jumaa 26 ga Yuni na shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa karin sabbin mutum 684 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka;

Lagos-259

Oyo-76

Katsina-69

Delta-66

Rivers-46

Ogun-23

Edo-22

Osun-22

Ebonyi-21

DUBA WANNAN: An kama wani fasto da bindigu masu yawa

FCT-20

Kaduna-16

Ondo-10

Imo-9

Abia-9

Gombe-5

Plateau-4

Bauchi-4

Ekiti-2

Anambra-1

Alkalluman da hukumar ta dakile cututtukan ta fitar a ranar Jumaa 26 ga Yunin shekarar 2020 ya nuna cewa jimillar wadanda suka kamu da cutar ta korona a kasar 23298.

An sallami mutum 8253 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 554.

A wani labarin, kun ji cewa jana'izar marigayi Ajimobi za a yi ta ne a tsakanin iyalansa, iyalan marigayi tsohon gwamnan jihar Oyo suka sanar kamar yadda dokokin dakile yaduwar cutar coronavirus take.

Mai magana da yawun tsohon gwamnan, Bolaji Tunji ya sanar da hakan a ranar Juma'a, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Tunji ya sanar da manema labarai hakan a garin Ibadan. Ya ce ba za a yi jana'izar ba a ranar Juma'a ba, kuma iyalansa kadai za su halarta.

Ya kara da cewa za a sanar da shirye-shiryen jana'izar daga baya.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Ajimobi ya rasu a ranar Alhamis a jihar Legas a asibitin First Cardiologist Consultant, asibitin kudi da ke jihar Legas.

Kwamishinan lafiya na jihar Legas, Farfesa Akin Abayomi ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi ya rasu sakamakon cutar coronavirus da ta kama shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel