Shugaba Buhari ya yi amanna da namijin kokarin da gwamna Zulum ke yi

Shugaba Buhari ya yi amanna da namijin kokarin da gwamna Zulum ke yi

Mai baiwa shugaban kasa shawara kan lamuran tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno (Mai ritaya), ya bayyana irin farin cikin da shugaba Buhari ke yi da gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum.

Monguno ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayinda ya kai ziyara Maiduguri, birnin jihar Borno.

Ya kai gaisuwar ta'azziya ne ga gwamnati da al'ummar jihar Borno bisa hare-haren Boko Haram na kwanakin nan inda akayi asarar rayuka da dama.

Monguno ya samu rakiyar ministar walwala, Sadiya Umar Farouq; shugaban hukumar leken asiri NIA, Ahmad Rufa'i Abubakar; da shugaban kwamitin hukumar Soji na majalisar dattawan Sanata Ali Ndume.

Sauran sune Sanata Yusuf. A Yusuf, da Hanarabul Hadiza Bukar Abba.

Shugaba Buhari ya yi amanna da namijin kokarin da gwamna Zulum ke yi
Shugaba Buhari ya yi amanna da namijin kokarin da gwamna Zulum ke yi
Asali: Twitter

KU KARANTA: Gwamnonin PDP 10 na shirin shigowa APC na da da dadewa ba - Yahaya Bello

Monguno yace: "Shugaban kasa da kansa ya shaida shekararka ta farko matsayin gwamnan jihar Borno. Irin kokarin da kake yi wajen kawar da wannan lamari, ya zama abin koyi ga al'ummar jihar Borno."

"Ka kai ziyara Abuja lokuta da dama domin ganin yadda gwamnatin jihar Borno da hukumomin tsaro za su iya hada kai wajen kawar da yan ta'adda."

"Muna tabbatar da maka da cewa shugaban kasa ya bamu umurni mu sake duba lamarin da kuma hanyoyin kawo karshen wannan halin da al'ummar jihar Borno suka samu kansu."

A nasa martanin, gwamna Babagana Umara Zulum ya yabawa shugaba Muhammadu Buhari kan kyakkyawar niyyarsa wajen kawo karshen ta'addanci a Arewa maso gabashin Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel