Gwamnonin PDP 10 na shirin shigowa APC na da da dadewa ba - Yahaya Bello

Gwamnonin PDP 10 na shirin shigowa APC na da da dadewa ba - Yahaya Bello

Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, ya ce kimanin gwamnonin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) 10 na hanyar sauya sheka All Progressives Congress (APC).

Ya bayyana hakan ne a hirar da yayi a shirin Politics Today na tashar Channels da yammacin Juma'a.

Yayinda yake amsa tambaya kan shin jam'iyyar APC zata ruguje idan shugaba Muhammadu Buhari ya fita daga jam'iyyar? Yahaya Bello ya ce hakan ba zai yiwu ba.

Yace: "APC na kara karfi, kuma kamar yadda na fada, za a ga zahirin haka nan da yan kwanaki ko makonni masu zuwa a jihar Edo, Ondo, Anambara, Ekiti da Osun."

"Abin takaici ne takwaranmu, dan uwana kuma siriki na, Obaseki ya bar mu, amma a matsayinmu na yan jam'iyya, zamu kwato shi."

"Ina mai fada maka cewa akwai kimanin gwamnonin PDP 10 dake shirin shiga APC kuma hakan zai faru nan ba da dadewa ba."

Gwamnonin PDP 10 na shirin shigowa APC na da da dadewa ba - Yahaya Bello
Yahaya Bello
Asali: UGC

KU KARANTA: Gwamnoni masu adawa da Oshiomole sun kaiwa Buhari ziyarar godiya (Hotuna)

Bayan haka, Yahaya Bello ya yi tsokaci kan raye-rayen da ake cewa an watsawa babban jagoran APC, Bola Tinubu, kasa a ido yan kwanakin nan.

Yace: "Sanata Bola Tinubu jagora ne, uba ne, kuma mu'asassin jam'iyyarmu. Ya bada gudunmuwa matuka wajen ganin jam'iyyar ta cimma matsayin da take yau."

"Babu wanda ya isa a jam'iyyar da zai raina babban jagora. Babu wanda ke raina shi. Har yanzu uba ne."

A bangare guda, wasu daga cikin ‘yan majalisar NWC ta jam’iyyar APC da aka ruguza a wajen taron NEC sun ce su na tuntubar Lauyoyi da masu ruwa da tsaki domin yanke shawara game da matakin da za su dauka.

Duk da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ja-kunnen ‘ya ‘yan APC a kan yi wa matakin da aka dauka kunnen-uwar-shegu, tsofaffin ‘Yan NWC sun nuna rashin gamsuwarsu da jam’iyyar.

Wadanda ke rike da shugabancin APC a da, sun fitar da jawabi cewa: “Mun lura cewa Victor Giadom ya kira kuma ya jagoranci taron NEC na jam’iyya, inda har aka dauki wasu matakai.”

“Yayin da NWC ta ke lura da takaddamar da ke faruwa, za ta tattauna da masu ruwa da tsaki da tarin Lauyoyi a game da matakin da za ta dauka na gaba.”

Wadanda su ka sa hannu a jawabin sun hada da: Hilliard Eta, Waziri Bulama da Lanre Issa-Onilu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel