Da duminsa: Barayin mutane sun koma hanyar Abuja-Kaduna, Sojoji sun ceci wasu fasinjoji daren jiya

Da duminsa: Barayin mutane sun koma hanyar Abuja-Kaduna, Sojoji sun ceci wasu fasinjoji daren jiya

Da alamun masu garkuwa da mutane sun koma babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna inda suka addabi matafiya a watanni baya kafin jami'an tsaro suka damke da dama cikinsu.

A ranar Alhamis, wasu fasinjoji sun tsallake rijiya baya yayinda Sojoji suka kai musu dauki ana gab da awon gaba da su.

Legit ta samu rahoto daga hedkwatar tsaro kan yadda jami'an Soji suka fitittiki masu garkuwa da mutanen cikin daji kuma dukkan fasinjojin da akayi kokarin sacewa na nan kalau.

A jawabin da hedkwatar ta saki, hukumar ta bayyana yadda jami'anta ke farautar yan bindigan.

Da duminsa: Barayin mutane sun koma hanyar Abuja-Kaduna, Sojoji sun ceci wasu fasinjoji daren jiya
Da duminsa: Barayin mutane sun koma hanyar Abuja-Kaduna, Sojoji sun ceci wasu fasinjoji daren jiya
Asali: Twitter

Jawabin yace: "Dakarun Operation THUNDER STRIKE ..sun kawar da yunkurin garkuwa da fasinjoji a hanyar Abuja zuwa Kaduna ranar 25 ga Yuni, 2020."

"Sakamakon rahoton mazauna kan yadda yan bindiga ke harkoki tsakanin Alheri Camp da kamfanin Olams dake hanyar Abuja-Kaduna, Sojoji suka afka wajen kuma suka yi artabu da yan bindigan."

"Sojojin sun galabesu da wutan annaru, idan suka hanasu iya cika manufarsu kuma suka gudu cikin daji a rikice."

"Yayinda Sojoji ke artabu, fasinjojin mota mai tafiya daga Abuja zuwa Kaduna kirar Toyota Hiace (Lagos MUS-944FR) da suka yi niyyar sacewa, sun tsere cikin dazukan dake wajen."

"Amma, jaruman sojojin suka fitittikesu cikin dajin kuma suka ji musu raunuka yayinda suke kokarin ceto fasinjojin da suka gudu cikin daji."

"Yanzu haka Sojojin suna bincike a yankin, suna farautar yan bindigan kuma ana sintiri a hanyar."

"Hakazalika an ga dukkan fasinjojin motar da aka kaiwa hari."

Kalli hotuna:

KU KARANTA Gwamnoni masu adawa da Oshiomole sun kaiwa Buhari ziyarar godiya (Hotuna)

Da alamun yan bindiga na kokarin komawa tada hayaniya a hanyar Abuja zuwa Kaduna duk da irin damke da dama cikinsu da jami'an yan sanda sukayi a watannin baya.

Wannan shine karo na biyu da yan bindiga zasu tare hanya kusa da kamfanin Olams. A farko sun yi awon daga da wasu daliban jami'ar Ahmadu Bello ABU shida.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng