Gwamnan APC ya cire takunkumin fuska bayan fitowa daga dakin ganawa da Buhari a Villa
Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ki saka takunkumin fuska a fadar shugaban kasa bayan kammala ganawa da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ranar Juma'a.
Saka takunkumin fuska na daga cikin matakan da gwamnatoci a matakin jiha da tarayya suka dauka domin dakile yaduwar annobar korona.
A yayin da sauran abokansa ke sanye da takunkuminsu na fuska yayin ganawa da manema labarai bayan kammala taro da shugaba Buhari, Bello ne kadai fuskarsa a bude, babu takunkumi.
Bello ya kafe kan cewa babu cutar korona a jiharsa, koda hukumar NCDC ta sanar da samun alkaluma daga jiharsa, ya kan zargesu da kitsa kitimurmura.
Sati uki da suka gabata, gwamna Bello ya saka dokar kulle a karamar hukumar Kabba/Bunu ta tsawon mako biyu bayan an tabbatar da samun mai dauke da kwayar cutar korona.
DUBA WANNAN: Sule Lamido ya ci gyaran Atiku a kan kalaman yabon jam'iyyar APC
Sai dai, gwamnan ya gimtse dokar bayan kwana hudu kacal tare da bayyana cewa babu cutar korona a jihar Kogi.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng