Gwamnoni masu adawa da Oshiomole sun kaiwa Buhari ziyarar godiya (Hotuna)

Gwamnoni masu adawa da Oshiomole sun kaiwa Buhari ziyarar godiya (Hotuna)

Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin shugaban kwamitin rikon kwaryar jam'iyyar All Progressives Congress APC da wasu gwamnoni a fadar Aso Villa yau Juma'a, 26 ga Yuni, 2020.

Gwamnonin wanda shahararrun masu adawa da tsohon shugaban APC Adams Oshiomole sun kai ziyarar domin yi ma Buhari godiya kan yadda ya shawo kan rikicin da ya kusa warware tsintsiyar jam'iyyar.

Daga cikin gwamnonin da suka kai ziyarar akwai gwamnan jihar Yobe kuma shugaban kwamitin rikon kwarya, Mai Mala Buni; da gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello.

Sauran sune gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello; da gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu.

Legit Hausa ta sami labari daga hadimin Buhari, Sallau Buhari, wanda ya wallafa a shafinsa na Tuwita

Yace: "Shugaba Buhari ya karbi bakuncin sabon shugaban kwamitin rikon kwaryar APC da wasu guda hudu da suka zo masa godiya."

"Buhari ya karbi Mai Mala Buni, gwamnan Neja, Ekiti, Kogi da Kebbi a ziyara nuna godiya da suka kai fadar shugaban kasa Abuja."

Kalli hotunan ziyarar:

Gwamnoni masu adawa da Oshiomole sun kaiwa Buhari ziyarar godiya (Hotuna)
Gwamnoni masu adawa da Oshiomole sun kaiwa Buhari ziyarar godiya (Hotuna)
Asali: Twitter

KU KARANTA: Lokacin mayar da dokar hana fita ya yi - Sakataren gwamnatin tarayya

Gwamnoni masu adawa da Oshiomole sun kaiwa Buhari ziyarar godiya (Hotuna)
Gwamnoni masu adawa da Oshiomole sun kaiwa Buhari ziyarar godiya (Hotuna)
Asali: Twitter

Gwamnoni masu adawa da Oshiomole sun kaiwa Buhari ziyarar godiya (Hotuna)
Gwamnoni masu adawa da Oshiomole sun kaiwa Buhari ziyarar godiya (Hotuna)
Asali: Twitter

A yau Alhamis, 25 ga watan Yuni Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattafa hannu an sallami daukacin Kwamitin gudanarwan jam’iyyar All progressives Congress APC.

Jam'iyyar APC ta yanke wannan hukunci ne a wurin taron Majalisar NEC da ake yi yanzu haka a babban birnin tarayya.

NEC wanda ita majalisar koli a jam’iyyar ta yi na’am da shawarar da shugaban kasa ya bada, ta ruguza majalisar NWC.

Ga jerin sabbin yan kwamitin rikon kwaryar:

Gwamnoni masu adawa da Oshiomole sun kaiwa Buhari ziyarar godiya (Hotuna)
Gwamnoni masu adawa da Oshiomole sun kaiwa Buhari ziyarar godiya (Hotuna)
Asali: Twitter

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Online view pixel