Gwamna da matarsa sun killace kansu bayan diyarsu ta kamu da cutar Korona

Gwamna da matarsa sun killace kansu bayan diyarsu ta kamu da cutar Korona

Gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, da maidakinsa, Edith Okowa, sun shiga killace kansu na tsawon kwanaki 14 bayan diyarsu ta kamu da cutar Coronavirus (COVID19).

Gwamnan ya sanar da hakan a shafinsa na Tuwita ranar Juma'a, 26 ga Yuni, 2020.

Okowa yace: "A yau din nan, Edith da ni mun samu labarin cewa daya daga cikin 'yayanmu mata ta kamu da cutar COVID19."

"Saboda haka, bisa ga ka'idojin da aka gindaya, zamu shiga killace kanmu na tsawon kwanaki 14."

Gabanin yanzu, sakataren gwamnatin jihar, Mista Chiedu Ebere da kwamishanan labaran jihar, Charles aniagwu, sun kamu da cutar Korona karshen makon da ya gabata.

Yanzu haka suna jinya a cibiyar killacewa a jihar, cewar sakataren yada labaran gwamna, Olisa Ifeajika.

Gwamna da matarsa sun killace kansu bayan diyarsu ta kamu da cutar Korona
Gwamna da matarsa sun killace kansu bayan diyarsu ta kamu da cutar Korona
Asali: UGC

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel