FG ta rufe gadar Kara da ke babban titin Legas-Ibadan

FG ta rufe gadar Kara da ke babban titin Legas-Ibadan

- Gwamnatin Tarayya za ta rufe babban gadan Kara da ke kan titin Legas zuwa Ibadan

- Za a rufe gadan ne domin yin gwajin ingancin cigaba da amfani da shi bayan gobarar da ya afku a ranar Lahadi

- Dan kwangilar da ke kula da aikin ya nemi a rufe gadan daga ranar Juma'a zuwa Lahadi

Bayan hatsarin tanka da ya yi sanadin rasuwar mutum biyu a kan gadan Kara da ke babban titin Legas zuwa Ibadan a ranar Lahadi, Ma'aikatan Ayyuka ta ce za a rufe hanyar don yin gwajin inganci.

Hakan na cikin wata wasika ne da Mataimakin Direktan sashin kula da Manyan hanyoyi na Ma'aikatan Ayyuka, K.Y. Ibrahim ya aike wa gwamnatin jihar Legas kamar yadda The Punch ta ruwaito.

FG ta rufe gadan Kara da ke babban titin Legas-Ibadan
FG ta rufe gadan Kara da ke babban titin Legas-Ibadan. Hoto daga The Punch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: An kama wani fasto da bindigu masu yawa

Ya nemi hadin kai da goyon bayan gwamnatin Legas domin samun nasarar aikin.

Ibrahim ya ce dan kwangilar da ke aiki a babban titin ya nemi a rufe gadan daga ranar Juma'a zuwa Lahadi domin "tabbatar da ingancin gadar bayan gobarar."

Wasikar ta ce, "Muna neman taimakon Gwamnatin jihar Legas wurin magance cinkoson ababen hawan da za a samu yayin aikin da kuma taimako wurin kawar da motocin da suka yi hatsari a gadan."

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, wani magidanci mai shekara arba'in, Abdulrahaman Abdulkarim ya shiga hannun 'yan sanda a jihar Katsina saboda zarginsa da ake yi da kashe matarsa da jefa gawarta a cikin rijiya.

Ana zargin Abdulkarim ya aikata laifin ne a kauyen Madabu -Dabawa da ke karamar hukumar Dutsinma na jihar kamar yadda The punch ta ruwaito.

Mai magana da yawun 'yan sandan jihar, Gambo Isah ya tabbatar da afkuwar lamarin yayin da ya ke yi wa manema labarai jawabi a ranar Alhamis.

Ya ce wadda aka kashe, Wasila Sara, mai shekara 19, amaryar Abdulkarim ce.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel