Abiola Ajimobi ya mutu ne bayan COVID-19 ta jefa shi a gargara - Gwamna Fayemi

Abiola Ajimobi ya mutu ne bayan COVID-19 ta jefa shi a gargara - Gwamna Fayemi

Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti ya bayyana yadda halin lafiyar tsohon gwamnan Oyo, Sanata Abiola Ajimobi ya tabarbare bayan ya kamu da cutar Coronavirus.

Kayode Fayemi ya ce ya samu labarin lokacin da aka yi wa Abiola Ajimobi aiki a huhu. Fayemi ya ce ya ji dadin samun labarin, daga baya kuma jikin dattijon ya sukurkuce.

Dr. Fayemi ya ce tsohon gwamnan na Oyo ya shiga gargara bayan ya fara samun lafiya. Amma a karshe Coronavirus ce ta yi sanadiyyar mutuwarsa bayan an yi masa aiki.

Ajimobi ya yi aiki tare da Kayode Fayemi a lokacin da dukkaninsu su ke gwamnonin jihohinsu.

Haka zalika Bolaji Tunji wanda ya kasance mai taimakawa Abiola Ajimobi kan harkokin sadarwa da tsare-tsare, ya rubuta takardar makoki domin tunawa da maigidan na sa.

Mista Bolaji Tunji ya bayyana cewa Ajimobi ya yi wata tafiya zuwa babban birnin tarayya Abuja, tun daga lokacin ya kwanta rashin lafiyar da ubangiji bai nufi zai tashi ba.

KU KARANTA: Abin da ya kashe Ajimobi - Gwamnatin Legas

Abiola Ajimobi ya mutu ne bayan COVID-19 ta jefa shi a gargara - Gwamna Fayemi
Abiola Ajimobi da Magajinsa
Asali: Twitter

“Kamar jiya ne aka kira Abiola Ajimobi a wayar salula cewa ya zo Abuja, domin ayi maganar jam’iyya. Bai yanke shawarar wadanda za su yi masa rakiya ba. Saboda jirgin kasuwa ne, bai da da-damar daukar mutane sosai. Sai ya tafi da dogarinsa kurum.” Inji Tunji.

“Ya fada mana a ofishinsa da ke Oluyole cewa zai yi sha’awar zuwa garin Abuja tun da ya zama mataimakin shugaban jam’iyyar APC. Dole ofishinmu ya koma Abuja. Ya sanya doguwar rigarsa da ya saba, da hula, kamar dai yadda ya ke shiga a gida ko da ya na atisayen safiya.”

“’Za mu bar gari karfe 2:00 na rana.’ Ya fada mana a wancan lokaci. Aka shirya masa jirgi domin ya tafi.” Inji Hadimin marigayin.

A cewar Tunji, Sanata Ajimobi garau ya ke a lokacin duk da shekararsa 70. “Ya kan yiwa kansa wasa ya kira kansa Baba 70.

“Da zai bar gida, mutane kadan su ka yi masa rakiya, ban taba tunanin cewa ganin karshe na yi masa ba.”

Hadimin ya ce ya rasa gane inda Ajimobi ya samo cutar COVID-19 domin sun kiyayye duk wasu ka’idoji. Ya kuma bayyana cewa sai da aka roki tsohon gwamnan ya karbi mulki a jam’iyya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel