'Yan sanda sun damke korarren dan sandan da ya kware wurin satar babur

'Yan sanda sun damke korarren dan sandan da ya kware wurin satar babur

- Rundunar 'yan sandan jihar Bauchi ta bayyana damke wani korarren dan sanda a kan laifin satar babura

- Korarren dan sandan mai mukamin sajan ya shiga hannun jami'an tsaro ne bayan korafin da mutane ke kaiwa a kan titin Dass

- Dan asalin jihar Gomben mai suna Makama Musa mai shekaru 34 ya shiga hannu a ranar 24 ga watan Yunin 2020

Korarren dan sandan da ya kware a satar babura ya shiga hannun jami'an tsaro a jihar Bauchi.

Rundunar 'yan sandan jihar Bauchi ta damke wani korarren dan sanda mai mukamin sajan mai suna Makama Musa mai shekaru 34, bayan aikata fashi da makami da yayi.

An kama dan asalin jihar Gomben a ranar 24 ga watan Yunin 2020.

Kamar yadda rundunar 'yan sandan ta bayyana ta bakin kakakinta, DSP Ahmed Mohammed Wakil, kungiyar 'yan sintiri da ke ofishin 'yan sanda da ke Yelwa a jihar Bauchi ne suka damke Musa.

Wakil ya bayyana cewa an kama korarren sajan Musa sanye da kayan 'yan sanda a kan hanyar Dass bayan korafe-korafen da suka dinga samu.

"Wanda ake zargin ya amsa laifinsa bayan kama shi da aka yi sanye da kayan 'yan sanda tare da babur mai lambar rijista DBM-319-UR, Bauchi," yace.

Ya kara da cewa, "kwamishinan 'yan sandan jihar ya bada umarnin mika binciken laifinsa sashin bincike na musamman inda daga nan za a mika shi gaban kuliya."

'Yan sanda sun damke korarren dan sandan da ya kware wurin satar babur
'Yan sanda sun damke korarren dan sandan da ya kware wurin satar babur. Hoto daga Linda Ikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Jirwaye: Magu ya yi martani mai zafi bayan zargin Malami

A wani labari na daban, wata kotun majistare da ke jihar Osun a ranar Alhamis ta yankewa Oga Joseph mai shekaru 21 hukuncin shekaru biyar a gidan gyaran hali a kan yin amfani da 'mabudin sihiri' wurin bude motocin jama'a.

Mai shari'a Muhibah Olatunji ta kama Joseph da laifukan da suka hada da sata.

A yayin rokon rangwame a gaban kotun, ya bayyana yadda yake amfani da mabudin sihiri wurin bude motoci tare da sacesu.

Olatunji ta ce sakin wanda ake zargin ba zai kara wa al'umma komai ba sai dai karin hargitsi.

Alkalin ta ce wannan hukuncin zai gyara wanda aka kama da laifin tare da bashi damar koyon sana'o'i da zai amfana da su bayan fitowa daga gidan gyaran halin sannan hakan zai zama izina ga wasu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel