Yadda 'yan fashi suka bindige dan uwansu har lahira yayin sata

Yadda 'yan fashi suka bindige dan uwansu har lahira yayin sata

Wani da ake zargi da aikata fashi da makami ya bindige dan uwansa har lahira yayin da suke kokarin tserewa daga inda suka yi fashi da makami.

Lamarin ya faru ne a unguwar Oktitipupa da ke jihar Ondo kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Wasu da abin ya faru a idonsu sun ce 'yan fashin sun yi wa wani mai sana'ar hada-hadar kudi ta POS fashi ne kuma suka juya za su tsere amma mutumin ya musu ihun a tare.

Wannan ihun da mutumin ya yi ne ya jawo hankulan mutanen unguwar kuma suka bi sahun 'yan fashin a guje.

Yadda 'yan fashi suka bindige dan uwansu har lahira yayin sata
Yadda 'yan fashi suka bindige dan uwansu har lahira yayin sata. Hoto daga The Nation
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Bidiyon yadda wani dan Najeriya da ya diro daga bene hawa 9 kuma bai mutu ba

A yunkurin su na razana mutanen da ke binsu, daya daga cikin 'yan fashin ya yi yunkurin yin harbi a sama amma ya yi kuskure harsashin ta samu dan uwansa a kai.

Wadanda lamarin ya faru a idanunsu sun ce yan sanda daga caji ofis na Okitipupa sun kwato bindigu biyu tare da jakar kudi da suka sace daga hannun mai sana'ar ta POS daga hannun dan fashin da ya fadi matacce.

An kuma ce daga bisani yan sandan sun yi nasarar damko sauran 'yan fashin da suka yi yunkurin tserewa.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Ondo, ASP Tee-Leo Ikoro, ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce asirin 'yan fashin ne ya tonu kuma suka gamu da sakamakon abinda suke aikatawa.

A wani labarin, kun ji cewa yan bindiga a yammacin ranar Talata sun kai hari kauyen Karare da ke karamar hukumar Batsari a jihar Katsina inda suka sace diyar dagajin kauyen, Ciroma Ahmadu Karare.

Mazauna kauyen sun ce 'yan bindigan sun sace matashiyar mai shekaru 20 tare da wata mata mai shekara 23 da ke da goyo a bayanta a lokaci da aka yi awon gaba da su kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Yan bindigan da aka ce adadinsu ya kai 20 sun isa kauyen ne a kan babura dauke da bindigu kamar yadda suka saba.

Rahotanni sun ce sun bi gidaje da dama suna yi wa mutane fashi ciki har da gidan dagajin kauyen inda suka sace diyarsa.

Daya daga cikin mazauna kauyen, Mustapha Ruma ya ce yan bindigan sun kwace wayar dagajin kauyen sannan suka ba shi sabon layin waya.

Sun umurci ya kira su domin tattauna abinda zai biya domin fansar diyarsa. Yan bindigan kuma sun sace wasu dabobi da kayan abinci daga wurin mazauna kauyen yayin harin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel