An kama wani fasto da bindigu masu yawa

An kama wani fasto da bindigu masu yawa

'Yan sandan jihar Delta sun tabbatar da kama wani fasto na cocin Christ Holy Church, Asaba, Mr Fidelis Nwansa da aka samu da bindigu har guda shida.

Mai magana da yawun rundunar, DSP Onome Onovwakpoyeya, ya tabbatar da afkuwar lamarin yayin hira da manema labarai a ranar Alhamis a garin Asaba.

Kakakin 'yan sandan ya bayyana cewa bayan an damke shi, faston ya yi ikirarin yana aiki tare da wata kungiyar 'yan banga ne a Anambra.

An kama wani fasto da bindigu masu yawa
An kama wani fasto da bindigu masu yawa. Hoto daga The Nation
Asali: UGC

KU KARANTA: Bidiyon yadda wani dan Najeriya da ya diro daga bene hawa 9 kuma bai mutu ba

A cewar, Onovwakpoyeya, tuni rundunar ta fara cikakken bincike a kan lamarin domin gano ainihin dalilin da yasa ya mallaki bindigun.

"Jami'an mu sun kama wani fasto tare da bindigu shida. 'Yan sandan sun kuma kama wani shugaban kungiyar 'yan banga mai suna Freeman.

"An gano bindigun shida ne cikin wani kango da ke harabar cocin a garin Asaba.

"Bayan kama shi, faston ya yi ikirarin cewa yana aiki tare da wata kungiyar 'yan banga a Anambra kuma yana amfani da bindigun ne domin kare cocinsa.

"Amma a halin yanzu mun fara gudanar da binciken kwaf kwaf domin tabbatar da gaskiya a kan ikirarin da mutumin ya yi," in ji DSP Onovwakpoyeya.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, 'yan sandan birnin tarayya Abuja sun kama kasurgumin mai garkuwa da mutane, Bello Saleh na kauyen Dobi da ke karamar hukumar Gwagwalada da aka dade ana nema ruwa a jallo.

A sanarwar da kakakin rundunar, DSP Anjuguri Manzah ya fitar, ya ce an kama wanda ake zargin ne a mabuyarsa da ke kauyen Paiko Kore na karamar hukumar Gwagwalada.

DSP Manzah ya ce wanda ake zargin da 'yan tawagarsa sun harbe wani Ejike Idoko mazaunin kauyen Dobi har lahira a yayin da ya yi kokarin hana su tafiya da matarsa mai juna biyu.

Ya ce ana cigaba da kokarin ganin an kamo sauran 'yan tawagar na Saleh tare da kwato bindigun da ke hannunsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel