Da dumi-dumi: Karin mutum 594 sun kamu da korona a Najeriya

Da dumi-dumi: Karin mutum 594 sun kamu da korona a Najeriya

Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa a Kasa (NCDC) ta sanar da cewa annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 594 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 11.47 na daren ranar Alhamis 25 ga Yuni na shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa karin sabbin mutum 594 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka;

Lagos-159

Delta-106

Ondo-44

FCT-34

Edo-34

Oyo-33

Kaduna-33

Enugu-28

Katsina-25

DUBA WANNAN: An kama kasurgumin mai garkuwa da mutane, Bello Saleh

Imo-22

Adamawa-15

Ogun-12

Osun-11

Abia-8

Rivers-6

Nasarawa-5

Bauchi-5

Niger-5

Kebbi-4

Ekiti-3

Plateau-1

Taraba-1

Alkalluman da hukumar ta dakile cututtukan masu yaduwa ta fitar a ranar Alhamis 25 ga Yunin shekarar 2020 ya nuna cewa jumullar wadanda suka kamu da cutar ta korona a kasar 22,614.

An sallami mutum 7822 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jumullar mutane 549 a jihohi daban daban na kasar.

A wani labarin daban, Yan sandan birnin tarayya Abuja sun kama kasurgumin mai garkuwa da mutane, Bello Saleh na kauyen Dobi da ke karamar hukumar Gwagwalada da aka dade ana nema ruwa a jallo.

A sanarwar da kakakin rundunar, DSP Anjuguri Manzah ya fitar, ya ce an kama wanda ake zargin ne a mabuyarsa da ke kauyen Paiko Kore na karamar hukumar Gwagwalada.

DSP Manzah ya ce wanda ake zargin da 'yan tawagarsa sun harbe wani Ejike Idoko mazaunin kauyen Dobi har lahira a yayin da ya yi kokarin hana su tafiya da matarsa mai juna biyu.

Ya ce ana cigaba da kokarin ganin an kamo sauran 'yan tawagar na Saleh tare da kwato bindigun da ke hannunsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel