Jerin shawarwari 4 da majalisar zartaswan APC ta yanke yau

Jerin shawarwari 4 da majalisar zartaswan APC ta yanke yau

Bayan rikicin da ya barke tsakanin mambobin kwamitin gudanarwan jam'iyyar All Progressives Congress APC bayan hukuncin kotun daukaka kara ta tabbatar da dakatad da shugaban uwar jam'iyyar, Adams Oshiomole, shugaba Buhari ya sa baki.

Kafin sa bakinsa, mafi akasarin mambobin kwamitin gudanarwan sun zabi Sanata Abiola Ajimobi matsayin shugaban riko, amma lokacin yana kwance a asibiti.

Daga baya aka baiwa Hanarabul Hillard Eta rikon kwarya madadinsa.

A bangare guda kuwa, mataimakin sakataren jam'iyyar, Victor Giadom, ya yi ikirarin cewa shine sahihin shugaban jam'iyyar saboda kotu ta yanke hukuncin haka,

Domin raba gardama, Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da mataimakin sakataren Victor Giadom, a matsayin sahihin mukaddashin shugaban uwar jam'iyyar bayan kwashe kwanaki yana lura da lamarin a dokance.

Legit Hausa ta samu labarin hakan daga mai magana da yawun shugaba Buhari, Malam Garba Shehu da yammacin Laraba, 24 ga Yuni, 2020.

Buhari ya kara da cewa saboda haka zai halarci taron majalisar zartaswar jam'iyyar da Giadom ya shirya ta yanar gizo.

KU KARANTA: Tsohon shugaban jam'iyyar APC na rikon kwarya, Abiola Ajimobi, ya mutu

Jerin shawarwari 4 da majalisar zartaswan APC ta yanke yau
Jerin shawarwari 4 da majalisar zartaswan APC ta yanke yau
Asali: Twitter

A taron da ya gudana yau Alhamis a fadar shugaban kasa, majalisar zartaswar ta yanke shawari hudu.

Ga jerin shawarin:

1. A janye dukkan kararraki daga kotu

An umurci dukkan 'yayan jam'iyya su janye dukkan kararrakin da suka shigar kotu kan juna da jam'iyyar. Cikin mako daya kacal, mambobin jam'iyyar sun rika safa da marwa a kotuna daga Abuja zuwa Kano zuwa Rivers d.s.s kawai don samun nasara kan juna.

A yanzu, an yanke shawarar a zauna lafiya kuma kada wanda ya sake zuwa kotu

2. An rusa kwamitin gudanarwan jam'iyyar

Da amincewar shugaba Buhari, an rusa kwamitin gudanarwar jam'iyyar NWC karkashin jagorancin Adams Oshiomole.

3. An nada kwamitin rikon kwarya

Bayan rusa kwamitin NWC, an nada gwamnan jihar Yobe matsayin shugaban jam'iyyar na rikon kwarya tare da mambobi 12 kuma an umurcesu su shirya taron gangamin jam'iyyar cikin watanni shida masu zuwa.

Daga cikin amabobin kwamitin rikon kwarya akwai gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello; gwamnan Osun, Gboyega Oyetola; Sanata Ken Nnamani, David Lyon Dss.

4. An tabbatar da sihhancin zaben fiddan gwanin gwamnan jihar Edo

Majalisar zartaswar ta amince da zaben fiddan gwanin gwamnan jihar Edo da Osaze Ize-Iyamu ya lashe duk da cewa an so a rusa.

An yi ittifakin cewa an gudanar da zaben fidda gwanin cikin lumana kuma an yi adalci saboda haka ba sai an rusa ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel