Hushpuppi: Jerin abubuwa 8 da aka kama tare da shahararren dan damfarar duniya
'Yan sandan kasar Dubai sun lissafa kayayyakin da suka samu yayin da suka kai sumame suka damke shahararren wanda ake zargi da damfara, Raymond Abass da aka fi sani da Hushpuppi da wasu.
'Yan sandan na Dubai a ranar Alhamis sun wallafa faifan bidiyo a shafinta inda ke nuna yadda aka kama Hushpuppi, dan Najeriya mazaunin Dubai a gidansa da ke Dubai.
Bidiyon ya tabbatar da kama Hushpuppi da yan tawagarsa yayin wani atsiaye da aka yi wa lakabi da “Fox Hunt 2”. An kama shi ne tare da wasu mutum 12 kamar yadda bidiyon ya nuna.

Asali: UGC
Laifukan da ake zarginsa da aikatawa sun hada almundahar kudi, yaudarar mutane don samun lambobin sirri, zambar banki, yin sojan gona, kuste ta intanet da sauransu.
Ga dai jerin abubuwa takwas da yan sandan suka bayyana a cikin faifan bidiyon da suka wallafa.
1. Ya yi damfara ta kudi da ya kai dirhami biliyan 1.6 ($435,611,200).
2. Yan sandan na Dubai sun kwace kudi kimanin dirhami miliyan 150 ($40,838,550) yayin sumamen.
3. Kwafuta laptop guda 21
4. Wayoyin salula 47
DUBA WANNAN: Hamshakin biloniyan Najeriya ya shirya angwancewa da diyar Trump
5. Naurar ajiye bayanai wato flash drive 15
6. Naurar ajiye bayanai na hard drive 5
7. Ya damfari mutane 1,926,400
8. Motoccin alfarma 13 da kudinsu ya kai dirhami miliyan 25 ($6,806,425).

Asali: UGC
Hushpuppi da yan tawagarsa sun damfari mutane da dama a sassa daban daban na duniya.
Sun kware wurin kirkirar shafin intanet na bogi don karkatar da kudaden da mutane ke biya ta intanet.
Yin kutse cikin imel din kamfanoni da aika sakon bogi ga abokan huldan kamfanoni domin yaudarar su.
Ga bidiyon sumamen a kasa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng