Muhimman abubuwa 11 da ya dace ku sani game da Ajimobi
Tsohon gwamna kuma Sanata na jihar Oyo, Abiola Ajimobi ya rasu a ranar Alhamis 25 ga watan Yunin shekarar 2020 sakamakon cutar COVID-19 wato coronavirus.
Ga wasu muhimman abubuwa 11 da ya kamata ka sani game da Abiola Ajimobi kamar yadda The Nation ta wallafa.

Asali: UGC
1. An haifi Abiola Ajimobi ne a ranar 16 ga watan Disamban shekarar 1949 a Oja-Iba a Ibadan.
2. Kakansa basarake na Sobaloju na Ibadan. Mahaifinsa, Pa Ajimobi, shima dan majalisa ne a tsohuwar shiyar Yamma kuma kawunsa, Hon. N.A. Ajimobi tsohon ministan Ayyuka da Sufuri ne a shiyar ta Yamma.
3. Yayi karatunsa na frimari a Saint Patricks School, Oke-Padre kuma ya kammala frimari a City Council Primary School Aperin.
Ya yi karatun sakandare a Lagelu Grammar School. Yana cikin dalibai masu hazaka wurin wasanni kamar kwallon kafa, guje-guje da sauransu.
4. Ajimobi ya yi karatun digiri na farko a State University of New York a Buffalo a Amurka. Ya yi digirinsa na biyu a Governors State University, Illinois.
5. Ajimobi ya auri Florence Ajimobi a shekarar 1980 kuma sun haifi yara biyar. Diyarsa ta farko Abisola Kola-Daisi 'yar kasuwa ce wacce ta kafa kamfanin Florence H Luxury.
6. A 2003, Ajimobi ya zama Sanata a Najeriya. Ya rike mukamin mataimakin shugaban marasa rinjaye.
DUBA WANNAN: Hamshakin biloniyan Najeriya ya shirya angwancewa da diyar Trump
A 2007, ya yi takarar gwamna a karkashin jam'iyyar APC amma bai yi nasara ba. Ya sake takara a 2011 a karkashin jam'iyyar ACN kuma ya lashe zabe.
7. Ya sake yin takarar gwamna karo na biyu a Afrilun 2015 a karkashin jam'iyyar APC inda ya yi nasara. Ajimobi shine gwamna na farko da ya fara yin tazarce a jihar.
8. An zabi Ajimobi a matsayin sanata a karkashin jam'iyyar APC a ranar 28 ga watan Satumban 2018 inda ya wakilci Oyo mazabar Oyo ta Kudu.
9. A ranar 9 ga watan Maris ne 2019, Ajimobi ya rasa kujerarsa ta sanata inda ya sha kaye hannun Kola Balogun na jam'iyyar PDP.
10. A ranar 17 ga watan Yunin 2020, Kwamitin Gudarwa, NWC na jam'iyyar APC ta zabi Ajimobi a matsayin shugaban riko na jam'iyyar.
11. A ranar 18 ga watan Yunin 2020, an yada jita-jita cewa Ajimobi ya rasu amma daga bisani aka gano ba gaskiya bane.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng