Yanzu-yanzu: Tsohon shugaban jam'iyyar APC na rikon kwarya, Abiola Ajimobi, ya mutu

Yanzu-yanzu: Tsohon shugaban jam'iyyar APC na rikon kwarya, Abiola Ajimobi, ya mutu

Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Tsohon gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobo, ya rigamu gidan gaskiya, Punch ta ruwaito.

Tsohon gwamnan ya mutu ne yana mai shekaru 70 bayan fama da muguwar cutar na ta Coronavirus.

Ajimobi, ya yi gwamnan jihar Oyo tsakanin shekarar 2011 da 2019, uma aka nadashi mataimakin shugaban jam'iyyar All Progressives Congress APC (Kudu).

Tsohon gwamnan ya yi jinya ne a asibitin First Cardiologist and Cardiovascular Consultants Hospital, dake Legas ranar 2 ga watan Yuni, 2020.

Daga baya ya warke daga cutar Koronar amma duk da haka bai daina jinya ba.

A kwantar da shi tare da matarsa, Florence, a asibitin amma ta samu sauki kuma aka sallameta.

Kamar sauran manyan masu kudi, Ajimobi ya yi jinyar cutar a asibitin kudi maimakon cibiyar killace masu cutar na gwamnati.

Allah ya jikansa da rahama.

KU KARANTA: Buhari ya zabi Alkalin Abuja, Usman Bello, matsayin dan takaran babban mukami a kotun duniya ICC

Yanzu-yanzu: Tsohon shugaban jam'iyyar APC na rikon kwarya, Abiola Ajimobi, ya mutu
Yanzu-yanzu: Tsohon shugaban jam'iyyar APC na rikon kwarya, Abiola Ajimobi, ya mutu
Asali: Depositphotos

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel