Buhari ya zabi Alkalin Abuja, Usman Bello, matsayin dan takaran babban mukami a kotun duniya ICC

Buhari ya zabi Alkalin Abuja, Usman Bello, matsayin dan takaran babban mukami a kotun duniya ICC

Shugaba Muhammadu Buhari ya zabi babban Alkalin kotun birnin tarayya FCT, Ishaq Usman Bello, matsayin dan takaran mukamin Alkali a kotun masu laifin duniya wato International Criminal Court (ICC).

Kotun ICC da aka bude a ranar 1 ga Yuli, 2002 wata kotu ce da ta game dukkan dokokin duniya kuma tana da daman hukunta masu laifin kisan game iyali, zalunci, da algungumanci.

Hedkwatan Kotun ICC na zaune a Hague, kasar Holan.

Duk da karfinta, kotun ba ta da hurumin hukunta dan kasar da bata cikin jerin kasashen da ke mamban kotun.

Ana bukatar kasashen duniya su zabi yan takaran da zasu kara a zaben kujeran Alkalin kotun guda shida.

Za'a gudanar da zaben ne a ranar 7 zuwa 17 ga Disamba, 2020 a hedkwatar majalisar dinkin duniya dake birnin New York, kasar Amurka.

Buhari ya zabi Alkalin Abuja, Usman Bello, matsayin dan takaran babban mukami a kotun duniya ICC
Buhari ya zabi Alkalin Abuja, Usman Bello, matsayin dan takaran babban mukami a kotun duniya ICC
Asali: Facebook

KU KARANTA: Tsohon shugaban jam'iyyar APC na rikon kwarya, Abiola Ajimobi, ya mutu

Buhari ya zabi Alkali Usman Bello, ya wakilci Najeriya a takarar zaben.

Bello ya zama lauya ne a shekarar 1983 kuma ya kwashe shekaru 35 yanzu yana bakin aiki.

A matsayinsa na shugaban Alkalan kotun birnin tarayya Abuja, ya bada karfi wajen rage yawan fursunoni a gidajen yarin dake Abuja.

Ya fara ziyartar gidajen gyara halin dake huruminsa kuma ya baiwa sama da fursunoni 40 yanci.

A Oktoban 2017, ministan shari'a, Abubakar Malami, ya nada shi shugaban kwamitin fadar shugaban kasa wajen rage yawan fursunoni da gyaran gidajen yarin Najeriya

Legit Hausa ta kawo muku rahoto ranar 4 ga Yuni cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zabi Ngozi Okonjo Iweala, a matsayin yar takarar kujerar darakta janar ta kungiyar cinikayya ta duniya (WTO), The Cable ta ruwaito.

Kamar yadda takardar da jaridar The Cable ta gani a ranar Alhamis, Buhari ya janye takarar Yonov Fredrick Agah, wakilin dindindin na Najeriya a WTO, a matsayin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng