Yanzu-Yanzu: Yan sanda sun bude sakatariyar APC, sabbin shugabannin sun shiga

Yanzu-Yanzu: Yan sanda sun bude sakatariyar APC, sabbin shugabannin sun shiga

Jami’an hukumar yan sanda sun bude hedkwatar uwar jam’iyyar All Progressives Congres APC dake unguwar Wuse 2, birnin tarayya Abuja, Punch ta shaida.

Hakan ya faru ne bayan majalisar zartaswar jam’iyyar karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta rusa kwamitin gudanarwar jam’iyyar da Adams Oshiomole ke jagoranta.

Sabon Shugaban kwamitin rikon kwarya da shirya taron gangami, Mai Mala Buni, ya shiga sakatariyar inda ya tattauna da ma’aikatan hedkwatar.

Yanzu-Yanzu: Yan sanda sun bude sakatariyar APC, sabbin shugabannin sun shiga
Yanzu-Yanzu: Yan sanda sun bude sakatariyar APC, sabbin shugabannin sun shiga
Asali: Twitter

KU KARANTA: Buhari ya zabi Alkalin Abuja, Usman Bello, matsayin dan takaran babban mukami a kotun duniya ICC

Yanzu-Yanzu: Yan sanda sun bude sakatariyar APC, sabbin shugabannin sun shiga
Yanzu-Yanzu: Yan sanda sun bude sakatariyar APC, sabbin shugabannin sun shiga
Asali: Twitter

Da safe, Legit Hausa ta kawo muku rahoton cewa 'yan sandan sun garkame sakatariyar jami'yyar APC na kasa kuma sun hana sakataren jamiyyar Arc Waziri Bulama shiga ofishinsa da ke cikin sakatariyar.

'Yan sandan dauke da bindigu da suka iso majalisar tunda safe cikin mota kirar Toyata Land Cruiser mai lamba Abj-140DN ne suka dakatar da Bulama.

Cikin mamaki, Bulama ya nemi ganin shugaban tawagar 'yan sandan kana daga bisani ya kira kwamishinan 'yan sanda na Abuja.

Ya shaidawa manema labarai cewa, "Na iso aiki da safe na tarar da yan sanda da suka ce an basu umurni daga sama su rufe sakatariyar."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel